TSARON AL'UMMA SHINE GABA DA KOMAI
Daga Hafiz Balarabe Gusau
Hakika dukkan Al'ummar da basu da wada taccen tsaro Al'umma ce dake da na kasu babba" domin kuwa hankali baya kwantuwa a cikinta, zaman lafiya yayi hannun riga a cikinsu, kullum baya zasu zama maimakon cigba da habaka.....................
Tashin hankali da kisan kare dangi da akeyiwa Al'umma a karkararmu, abun kullum kara ta'azzara yakeyi. Idan ka ganewa idanuwanka hanlin da jama'ar karkara suke ciki a Jihar Zamfara hanakali zai tashi matuka zakayi tunanin anya a kwai jami'in tsaro a jihar nan kuwa ko cikin kasar nan ma kuwa?
Dukkan mai tausayi zai tausayawa bayin Allah mazauna karkara dake cikin jihar Zamfara mu samman a wannan karnin.
Shin shugaban kasa *Muhammadu Buhari* ya san halin da Al'ummar jihar Zamfara ma suke ciki kuwa?
Shin ko shugaban kasa ya san adadin rayukan da aka kashe a cin wannan watan na azumin ramadan kuwa? Sun haura sama da mutum dari a jihar Zamfara wadanda basuji ba basu ganiba?
Shin kana damuwa kuwa a matsayinka na shugaban kasa da lamuran dake faruwa a jihar Gwamnan jiha da sauran wadanda keda ragamar tsaro sunyi biris da ragamar tsaro harkar siyasar su ke gabansu
Ya kuke ji lokacin da kuke barci a gidajen ku, ga rayuwar Al'ummar karkara a cikin hadarin bala'in da yakeyi musu juyin waina?
Ku sani Al'umma sun cire fargaba' saura jajircewa ce kawai ya rage Alumma zasuyi suyi maku kifar juyin waina a dan lokaci kalilan...
Comments
Post a Comment