YUNKURIN GWAMNATIN BUHARI NA KAMA OBASANJO



Daga Shafin Datti Assalafiy

BBC Hausa sun ruwaito labarin cewa tsohon shugaban Kasa Obasanjo ya bayyana zargin cewa shugaban Kasa Buhari yana shirin kamashi ta hanyar tattara shaidun boge...

Haba Obasanjo ai indai kana da gaskiya bai kamata ba ma ka bayyanawa duniya cewa ana shirin kama ka, sai ka bari idan har an kama ka gaskiyarka ta kubutar dakai idan kana da ita

Muna kara tunatar da shugaba Buhari a tuntubi Obasanjo naira biliyon ko miliyon nawa ya baiwa su Abubakar Shekau lokacin da yaje garin Maiduguri ta'aziyar mutuwar shugaban kungiyar Boko Haram na farko Muhammad Yusuf
Ko da yake a lokacin Abubakar Shekau sojoji sun harbeshi a kafa ya boye a wani gida cikin garin Maiduguri kafin suka sulale dashi zuwa Kano inda yayi jinyar harbin da aka masa, watakila da irin kudin da Obasanjo ya basu aka yiwa Shekau jinya kafin shigarsa jejin Sambisa karshen shekarar 2012

Allah Ka shiga tsakaninmu da miyagun mutane azzalumai 'yan kwangilar rusa arewa da sunan Boko Haram

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA