KIMANIN MATA DUBU BIYAR (5,000) SUKA AMFANA DA KYAUTAR ATAMFOFI DAGA MATAIMAKIN GWAMNAN ZAMFARA MALAM IBRAHIM WAKKALA


Kimanin mata marasa galihu Dubu Biyar (5000) suka amfana da tallafin atamfofi daga mataimakin gwamnan Zamfara Malam Ibrahim Wakkala Muhammad Liman domin cin bukukuwan sallah.

Mataimakin Gwamnan ya bayar da tallafin ne a gidan sa da ke cikin unguwar Albarkawa dake cikin Shelkwatar Jahar.

Da yake bayani wajen bada wannan tallafin, shugaban wata kungiya mai suna Wakkala Media Forum Alhaji Bello Ibrahim Gusau (Alhajin APC) yace; karancin abun dake shiga hannun Mataimakin Gwamna bai taba gadar ma shi da zuciyar talaucin kasa taimakon talakka gwargwadon hali ba. Haka kuma yace bai kwaikwayo sannan baya gasa acikin ayukkan alhairi da manufar burge talakka amma ya kanyi tarayya da masu zuciya irin ta shi ta son taimakon talakka ganin ya samu sa'ida.

Shima a nashi bayanin, Shugaban kula da shafin sada zumunta na na facebook na kungiyar Wakkala Media Forum wato Alhaji Ibrahim Bello Gusau (IBG) yace so da shaukin ganin talakka ya samu sa'ida yasa har uwayen mu mata bai zubar da su ba, duk da wannan ba shine karon farko da yake aiwatar da irin wannan gagrumin aikin alhairi ba.


IBG ya kara da cewa wannan na daga cikin dubban dalilan da muke kafa hujja da su cewa matukar shine jagoran al'umma jahar zamfara a 2019,  al'umma zasu samu sawaba a hannun shi.

Wakilin mu da ya zanta da daya daga cikin wadanda suka amfana da wannan tallafin tace; wannan ba shine karon farko ba na amfana da wannan tallafin ta kuma yi addu'a zuwa ga Mataimakin gwamnan da Allah ya biya mashi bukatun shi na alkahairi baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA