ITA DAI WANNAN RAYUWA ABAR TSORO CE KUMA BABBAN DARASI GA MASU HANKALI
Daga Shafin Datti Assalafiy
Tsohon gwamnan jihar Pilato Joshua Dariye kuma sanata mai ci a jam'iyyar APC kotu ta yanke masa hukuncin shekaru 14 a gidan yari sakamakon sace dukiyar jihar da yayi lokacin yana mulki, saura Jonah Jang insha Allah (Yaa Allah Ka jikan musulmin jihar Pilato wadanda akayiwa kisan ta'addanci aka gasa namansu akaci akayi video aka nunawa duniya saboda tsabagen nuna isa da samun daurin gindin gwamnoninsu) Allah dai ba azzalumin bawanSa ba.
Kuma wannan hukunci da kotu ta yanke masa kamar raddi ne ga 'yan adawa wadanda suke cewa gwamnatin Baba Buhari bata tuhumar 'ya'yan jam'iyyarta na APC sai na jam'iyyar adawa, yanzu kuma ko me 'yan adawa zasuce oho?
Ace mutum ya gama Gwamna, yana matsayin sanata maici, ya mallaki komai da dukiya karshe ya kare a wannan matsayi har da zubar da hawaye a idon duniya watakila a gidan yari za'a mutu, to babban abin kunya ne da tozarta gareshi
Gwamnatin Baba Buhari ba sani ba sabo wannan shine adalci, muna kira ga kowa yazo ya goyi bayan gwamnatin Baba Buhari Maigaskiya, wannan bawan Allah shugabanci yake gudanarwa tsakaninsa da Allah gwargwadon abinda ya bayyana a gareshi, yana yawan nanata cewa "duk wanda yaci amanar al'umma muka ganoshi ba zamu taba kyalewa ba sai ya amayar.."
A Kasa irin Kasarmu Nigeria da kusan kowa ya fitar da rai da tsammani akan tsarin gudanar da Kararraki da shari'ah na kotunan Kasarmu Nigeria da yanke hukunci na adalci kusan ba'ayi a gwamnatocin baya; yau an wayi gari a Nigeria kusan lokaci daya kotu ta yanke hukunci a kan tsoffin gwamnonin jihohi (Taraba da Pilato), imba a gwamnatin adalci na Baba Buhari ba ni kaina ban taba tsammanin zamu samu wannan gagarumin cigaban ba a harkan shari'a na adalci da yanke hukunci
Insha Allahu a hankali lamura zasu gyaru su daidaita a wannan Kasa tamu mai albarka karkashin jagorancin shugaba mai kwatanta gaskiya da adalci Muhammadu Buhari 'dan albarka irin albarka.
Yaa Allah Ka cigaba da agaza masa Ka tsaremu tare dashi daga dukkan sharrin bil'adama da aljan.

Comments
Post a Comment