Attajirin da ake zargi da yanka dubban mutane a Rwanda zai gurfana a kotu.
Daya daga cikin manyan mutane na karshe da ake zargi a kisan kiyashin da aka yi a Rwanda a 1994 zai gurfana a gaban kotun duniya da ke birnin Hague a ranar Alhamis. Felicien Kabuga na fuskantar tuhumar aikata kisan kiyashi da laifukan cin zarafin bil-Adama, a kan irin rawar da ake zargin ya taka wajen yanka 'yan kabilar Tutsi da 'yan Hutu masu sassaucin ra'ayi har dubu dari takwas (800,000). A farkon gurfanarsa gaban kotun a 2020, lauyoyin Mista Kabuga, sun musanta laifukan da ake tuhumarsa da su. Ana sa ran ya gurfana da kansa a gaban kotun ta duniya a zaman na Alhamis. Tsawon gomman shekaru Felicien Kabuga ya kasance daya daga cikin mutanen da ake nema a duniya ruwa a jallo. Masu gabatar da kara sun ce Mista Kabuga na gudanar da wata tashar rediyo, wadda ta rika yada kalaman kyama da haddasa gaba, wadanda ake bayyana 'yan kabilar Tutsi a matsayin kyankyasai tare da angiza 'yan Hutu kan su hallaka su duk inda suka gansu. Ana kuma tuhumar mutumin da ya taba kasanc...