DAN A DAI DAITA SAHU YA HADU DA AJALIN SA A YAYIN DA YAKE GUDUN TSERE WA YANSANDA

 




Ana zargin wani direba Adai-daita Sahu ya gamu da ajalin sa, a safiyar Asabar  yayin da yake gudun tserewa ƴan sanda dake kula da bin dokar tsaftar Muhalli ta karshen wata wata da gwamnatin jihar ta tanadar.

Al'amarin dai ya faru ne a dai-dai gadar Ado Bayero da ake kira gadar Lado dake Gyadi-gyadi a jihar Kano.


Ganau sun shaida faruwar lamarin sunce, direban baburin Adai-daita Sahun ya ɗaukko kayan miya ne daga kasuwar ƴan kaba, inda a ƙoƙarin sa na gujewa ƴan sandan da suka biyo shi baburin ya kife wanda hakan yayi sanadiyyar rasa ran nasa.


Sai dai kuma har izuwa yanzu rundunar ƴan sandan Kano ba tace komai ba an tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sanda ta wayar tarho  amma bai dauki kira ko bada amsar sakon da ya  aike masa ba.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA