Yan Fashin Daji Sun Halaka Basarake Da Wasu Mutane 13 A Jihar Nejan Najer

 



Har yanzu dai ‘yan fashin daji na ci gaba da kai hare-hare da kisan jama’a a wasu yankuna na Jihar Nejan Najeriya, wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin kakar debe amfanin gona ke kawo jiki. 

Rahotanni daga yankin karamar hukumar Mariga mai Iyaka da Jihohin Zamfara da Kebbi na nuna cewa a karshen makon nan ‘yan fashin dajin sun hallaka basaraken garin Mohoro tare da wasu mutane kimanin 12, saboda basaraken yaki amincewa mutanen yankinsa su biya harajin da ‘yan bindiga suka dorawa mutanen yankin.

Gwamnatin Jihar Neja dai tayi Allah wadai da wannan mugun aiki, sakataren gwamnatin Jihar Nejan Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya ce sun tura karin jami’an tsaro a yankin, kuma ya zuwa yanzu hankali ya fara kwantawa a wajen.

Ita ma rundunar ‘yan sanda ta Jihar Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin, kuma kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Monday Bala Kuryas ya ce suna daukar mataki.

A yanzu dai akwai fargaba sosai musamman wajan debe amfanin gona a wadannan yankuna.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA