Taƙaddama ta ɓarke a APC bayan fitar da ƴan kwamitin yaƙin zaɓen 2023

 



Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi ƙarin haske game da cece-ku-cen da ake yi musamman a shafukan sada zumunta na internet kan jerin sunayen tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da ta fitar.


Ƙananan maganganu sun fara ɓulla ne bayan da aka ga babu sunayen wasu jiga-jigan jam'iyyar a cikin jerin sunayen, ciki kuwa har da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo - wani abu da masana ke ganin zai iya barin baya da ƙura.


Bala Ibrahim shi ne Daraktan yaɗa Labaran Jam'iyyar kuma ya ce ba lalle bane a ga sunan kowa da kowa a cikin jerin sunayen mambobin kwamitin saboda "an kafa kwamiti ne domin taimakawa, kuma ba wai ana nufin mutum ɗaya shi zai iya komai ba, inda ka ji an ce mataimaki, akwai wani sama da shi,"


"A wannan kwamiti an duba an ga babu sunan shugaban ƙasa?, idan akwai shugaban ƙasa, maganar mataimaki ya shigo ba ta taso ba," a cewar Bala Ibrahim.


A cewarsa, an kafa kwamitin domin tsara dabarun neman ƙuri'ar ƴan Najeriya saboda akwai buƙatar waɗanda sunayensu ba sa cikin kwamitin su karkatar da kansu ga ayyuka masu muhimmanci.


Ya ce akwai yiwuwar a samu sauye-sauye a Jam'iyyar - "bayan wannan kwamitin, akwai wasu ƙananan kwamatoci da za a kafa na shiyya-shiyya, akwai wasu waɗanda ba lalle bane a ga sunansu ɓaro-ɓaro cikin kwamiti, amma rawar da suke takawa tana da yawa, wataƙila sune fitilar da ke haska wa wannan kwamiti hanya ya ga inda zai bi."


Hangen masana kan turka-turkar

Tuni masana suka fara tsokaci game da wannan mataki da ya janyo turka-turka. Dr Abubakar Kari na Jami'ar Abuja a Najeriya ya ce ƙaramar magana za ta iya zama babba idan gaggan Jam'iyyar ba su yi da gaske ba.


"Jam'iyyar ba ta da zaɓi sai ta fito da dabaru da hanyoyin magance wannan abu, idan ba haka ba, zai yi mata illa a zaɓukan da suke ƙaratowa, a takaice irin illar da za a masa shi ne za a kakkaɓe masa magoya baya, za a yi amfani da batutuwa na addini a yi masa zagon ƙasa a sa mutane su ƙyamace shi suƙi zaɓensa." in ji masanin.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA