Attajirin da ake zargi da yanka dubban mutane a Rwanda zai gurfana a kotu.

 


Daya daga cikin manyan mutane na karshe da ake zargi a kisan kiyashin da aka yi a Rwanda a 1994 zai gurfana a gaban kotun duniya da ke birnin Hague a ranar Alhamis.


Felicien Kabuga na fuskantar tuhumar aikata kisan kiyashi da laifukan cin zarafin bil-Adama, a kan irin rawar da ake zargin ya taka wajen yanka 'yan kabilar Tutsi da 'yan Hutu masu sassaucin ra'ayi har dubu dari takwas (800,000).


A farkon gurfanarsa gaban kotun a 2020, lauyoyin Mista Kabuga, sun musanta laifukan da ake tuhumarsa da su.


Ana sa ran ya gurfana da kansa a gaban kotun ta duniya a zaman na Alhamis.


Tsawon gomman shekaru Felicien Kabuga ya kasance daya daga cikin mutanen da ake nema a duniya ruwa a jallo.


Masu gabatar da kara sun ce Mista Kabuga na gudanar da wata tashar rediyo, wadda ta rika yada kalaman kyama da haddasa gaba, wadanda ake bayyana 'yan kabilar Tutsi a matsayin kyankyasai tare da angiza 'yan Hutu kan su hallaka su duk inda suka gansu.


Ana kuma tuhumar mutumin da ya taba kasancewa daya daga cikin hamshakan attajiran Rwanda, da samar da kudade ga kungiyoyi masu dauke da makamai inda yake ba su adduna.


Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe mutum dubu 800 a tashin hankalin na kwana dari, wanda ya daidaita kasar da ke yankin tsakiyar Afirka, abin da ya girgiza al' ummar duniya.


Mista Kabuga ya shiga hannu ne a Paris shekara biyu da ta wuce bayan ya yi ta kullu-kurciya da jamian tsaro tsawon shekara 25.


A yanzu da girma ya kama shi, yana da kusan shekara 90 ba kadan, lauyoyinsa sun ce, a yanayin da yake yayi raunin da ba zai iya jure wa fuskantar sharia ba.


To amma alkalai sun ki yarda da hakan inda suka yanke shawarar ci gaba da gudanar da shariar, amma da takaitaccen zama.


Ana sa rana masu gabatar da kara su gayyato sama da shedu hamsin a shariar da ake ganin za ta dauki shekaru.


Mutanen da suka tsira daga wannan kisan kiyashi na kasar ta Ruwanda sun bukaci da a gaggauta yanke yin shari'ar domin tabbatar musu da adalci.


Suna ganin Mista kabugan zai iya rasuwa kafin a yanke hukunci a kama shi da laifi, wanda hakan zai kasance yam utu a matsayin wanda ba a kama shi da laifin ta'asara da ake zargi ya aikata ba, tamkar ya sha ke nan, suke gani.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA