Dubun Wani Dan Damfara Mai Canjawa Mutane ATM A Wajen Cirar Kudi Ta Cika A Kano.





Dubun wani matashi mai zamba a bakin ATM dake fadin jihar Kano ta cika a yayi da yayi yunkurin cire wasu kudi daga ATM din da ya canza daga hannun wani.



Shedun gani da ido sun ga wasu mutane suna ragargaza wannan matashin,  da suka tambaya sai ake bayyana masu abin da ke faruwa.


" Wannan da kuke gani, sune masu zuwa ATM machine suna yiwa mutane wayo su chanja musu ATM din su, su kewaya zuwa wajen masu POS suce cire kudaden dake cikin asusun ajiyar".


Ganau din ya kara da cewa, "sun zo wajen mu a Kundila, sun yi withdrawing 450,000 da dare, wayewar gari sai ga Jami'an Yan sanda daga daga CID sun zo an kama mu saboda wata Hajiya tayi korafin an chanja mata ATM an Kuma kwashe mata kudi har Miliyan daya da Ravi.


"Muna ta kokarin warware wannan matsalar da muka shiga sai Jiya da dare ya sake zuwa zai cire 150,000 da ATM na wani (Nasiru Hassan, access bank) dama mun gane shi nan aka kama shi, ba musu yace ga kudin mu 450,000 mu rufa masa asiri bai san za a zo bincike shagon mu ba da bazai zo yayi transaction a gurin mu ba."


A halin yanzu an damka shi ga Hukumar Yansanda domain hannunta shi ga sashen bincike na Hukumar domin zurfafa bincike

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA