YADDA TURAWA SUKE KOKARIN KAFA KASAR ISRA'ILA HAKA NE SUKA KAFA AMERIKA DA SAURAN WASU KASASHE




Malam Aminu Aliyu Gusau


Tun daga shekarar 1887 lokacin da turawa, musamman turawan Biritaniya, suka fara kawance da yahudawa a kan manufar kwace kasar Falasdinu, har zuwa yau , zamu ga cewa babbar manufarsu itace kwace kasar ta Falasdin baki daya da kore dukkan Falasdinawa daga cikinta.


Ma'ana dai itace dukkan tattaunawa da ake yi a Majalisar dinkin duniya da wadda kasashen turawa suke yi game da samar da wata kasar Falasdinawa gefen kasar yahudawa munafunci ne ba gaskiya bane. Dama kawai suke son samu domin su idar da aikin da suka fara na kawar da dukkan Falasdinawa daga dukkan kasar ta Falasdin.


Wannan hanya da turawa da yahudawa suke bi a Falasdin ba nan ne suka fara haka ba. Sun yi haka a wasu kasashe, suka kwace su daga mazaunansu na asali, ta hanyar kashesu da dannesu da korarsu.


Daga cikin irin wadannan kasashe da turawa suka shiga suka kashe mafi yawan mazaunansu, suka danne sauran, suka mayar da kasar tasu, akwai Amerika da Australiya da Greenland.


A Afrika ma sun yi kokarin yin haka a wasu wuraren amma basu ci nasara ba. Misali Faransawa sun yi kokarin kwacewa da mamaye kasar Aljeriya, sai dai 'yan Aljeriya sun kwaci kasarsu da 'yancinsu ta hanyar yaki mai zafi. Haka ta faru a kasar Rodeshiya inda turawan Biritaniya suka yi kokarin yin zaman dirshan amma 'yan kasar suka yi gwagwarmayar kwatar kai, suka sake wa kasar suna zuwa Zimbabwe.


A Afrika kasa ta karshe da ta 'yanta kanta daga mulkin danniya na wariyar launin fata ita ce Afrika ta kudu. Wannan tsarin wanda a karkashin shi turawa suka kwace kasar, suka ware bakar fata da suke asalin masu kasa suka dannesu suna yi masu wariyar launin fata ana kiran shi da turanci "Apartheid".


Irin wannan tsarin shine turawa da yahudawa suke aiwatarwa a Falasdin, amma a madadin wariyar launin fata - farar fata da bakar fata - to da sunan wariyar kabila ake yi a Falasdin - yahudawa da larabawa.


Al-muhim dai shine mu gane cewar abinda ke faruwa a Falasdin tsari ne na turawa da suka saba aiwatarwa a duniya. Suna amfani ne da yahudawa saboda su yahudawan sun riga sun rine sun zama turawa don tsawon zaman da suka yi a Turai .


A halin yanzu Falasdin ita ce kasa ta karshe a duniya inda ake da sauran wannan matsala ta mulkin mallaka, inda kuma Falasdinawa basu yarda a kwace kasarsu ba, suke ta gwagwarmaya. Sai kuma gashi mas'alar Masjidul Aqsa ta mayar da mas'alar ta addini. Duk da kuwa ko a maganar kasa muka tsaya to gwagwarmayar kariyar kasar musulunci daga kafurai, ko sake kwato ta daga hannunsu idan sun kwaceta, duka mas'aloli ne na addini.


Allah Ka basu nasara Amin.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA