WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA




Daga S. Sadiq, Gusau.



Wani abunda ba'a saba gani ba musamman ga musulmi Arewacin Najeriya shine yima mutum sujada, wanda idan aka samu irin hakan abun yake zama abun al'ajabi a wurin al'umma.

Lahadi 1 ga watan Satumba 2019 magoya bayan jam'iyyar APC suka kai ziyara tare da gaisuwar bangajiya ga tsohon Gwamnan Zamfara wato Abdulaziz Yari Abubakar bayan ya dawo daga aikin hajji.

Abunda ya bada mamaki shine yin sujada tare da fashewa da kuka da wani tsohon Danmajalisa yayi mai suna Hon. Mannir Gidan Jaja, wanda ya Wakilci Zurmi ta yamma a gwamnatin da ta gabata yayi yana rokon yafiya ga gwamnan domin canza jam'iyya da yayi daga APC zuwa PDP, inda ya bayyana cewa bai yi wanka ba da ma can a baya.

A bunciken da jaridar Tauraruwa tayi, ta gano cewa shi dai Hon. Mannir Gidan Jaja ya canza jam'iyya daga APC zuwa PDP a watan da ya gabata sai dai bai samu karbuwa ba  ga jam'iyyar PDP dalilin sa kenan na komawa tsohuwar jam'iyyar sa.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU