Yan Sanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Ahmad Gulak A Imo
Dubun gudajjen sojan da ke jagorantar hare-haren sari-ka-noken IPOB ya siffanta yadda ya kashe Ahmed Hula, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa.
Yan sanda sun cafke kwamandan kungiyar IPOB da ake zargi da kashe Ahmed Gulak, tsohon hadimin shugaban kasa a bangaren siyasa na zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Kakakin ’yan sandan Jihar Imo, CSP Michael Abattam, ya ce Las Kofur Nwangwu Chiwendu, wanda dubun tasa ta cika ya gudu ne daga aikin soja ya shiga kungiyar ’yan ta’addan.
A lokacin da aka yi holen sa a hedikwatar ’yan da ke Owerri a ranar Laraba, ya shaida wa ’yan jarida cewa ya shiga aikin soja a 2013, amma bayan ya samu kwarewa a fannin sarrafawa da gyaran manyan makamai, sai ya tsere a 2021 ya shiga kungiyar IPOB.
“Ya zama Kwamanda a reshen soji na IPOB (ESN) inda ya horas da ’yan kungiyar sama 1,000 kan sarrafa makamai da kai hare-haren ta’addanci.
“Ya amsa laifin kai hare-hare kan ofishoshin ’yan sanda da gine-ginen gwamnati a jihar nan,” in ji kakakin ’yan sandan.
Ya ci gaba da cewa gudajjen sojan mai shekara 34, wanda aka dade ana nema ruwa-a-jallo, kan sa yaransa su yi masa leken asiri kafin ya kai harin sari-ka-noke, sannan ya tsere zuwa wasu jihohi kafin dubunsa ta cika.
Comments
Post a Comment