SOJOJIN NAJERIYA SUN FATATTAKI YAN TA'ADDA A JIHAR ZAMFARA
Dakarun sojin Najeria sun samu nasarar fatattakar "Yan ta'adda a kauyen Malele dake Masarautar Dansadau a Karamar hukumar mulkin Maru dake Jihar Zamfara.
Rahotannin da muke samu daga kauyen sun nuna cewa a jiya Lahadi daruruwan maharan saman babura fiye da 400 sun dauki aniyar kai hare-hare a kauyen Malele da sauran kauyuka da ke zagaye amma hakan bai samu ba saboda dauki da Sojojin sama tare da taimakon na kasa da suka kai.
Mutanen kauyukan dake kusa da wurin da abun ya faru sun tabbatar da ganin gomman gawarwakin wadannan "Yan ta'addan tare da baburan da suka hau zuwa wajen kai wannan farmakin da bai samu nasara ba, haka kuma sun shedi ganin wadanda suka ji rauni a kan babura suna gudu.
Allah Ya cigaba da ba Sojojin Najeriya nasara.
Comments
Post a Comment