YAN MATA 5 DA AKA YI GARKUWA DASU SUN SAMU "YANCI
"Yan mata biyar da akayi garkuwa da su a garin Furfuri dake Karamar hukumar Bungudu dake Jihar Zamfara sun samu kubuta daga wadanda suka yi garkuwa dasu.
Yaran duka diyan tsohon Akawunta Janar ne ma Jihar Zamfara. Anyi garkuwa dasu ne a watan 3 na wannan shekarar.
Idan baku manta ba a watan Oktoba da ya gabata "Yanta'addar sun fitar da wani faifan bidiyon yaran tare da miyagun makamai suna barazanar jefa su cikin aikin ta'addacin idan ba'a biya kudin da suka nema a basu ba.
Comments
Post a Comment