TAKAITATTUN LABARAN SAFIYAR JUMA'A 4/11/2022 DAGA JARIDAR TAURARUWA HAUSA NEWS KARKASHIN KAMFANIN BELMO MEDIA CONSULT
✅Jami'an tsaro sun fara bincike kan gawarwakin matasa 10 da aka tsinta a Edo.
✅An Fara Gudanar Da Bincike Game Da Cin Zarafin Wani Dan Jarida Da Dan Majalisar Wakilan Najeriya Ya Yi.
✅Tinubu Zai Fara Kaddamar Da Yakin Neman Zabensa A Jihar Filato, Ranar 15 Ga Watan Disamba.
✅Dubban 'Yan Najeriya Ne Suka Samu Kulawa Daga Kungiyar Likitoci Dake Yawo Kasashen Duniya.
✅Idan Na Ci Zabe Zan Sayar wa Da 'Yan kasuwa Duka Matatun Mai Na Kasa – Atiku.
✅Ba Zan Yarda A Samu “Cabal” A Gwamnatinmu Ba – Atiku.
✅NEMA Ta Raba Kayan Abinci Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Borno.
✅An Gurfanar Da Magidanci A Kotu Kan Daba Wa Surukinsa Kwalba.
✅An Kama Matashin Da Ya Yi Garkuwa Sannan Ya Kashe Yaro Mai Shekara 5 A Kano.
✅Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 44 A Arewacin Najeriya.
✅Gwamnati Ba Ta Sayen Makamai A Wajenmu – Kamfanin Sarrafa Makamai Na Najeriya.
✅Mun Lalata Haramtattun Matatun Mai Sama Da 70 Cikin Mako 2 – Sojoji
✅Miyagun Kwayoyi: NDLEA Ta Cafke Mutum 130 A Kaduna.
✅Dalibai 3,000 Sun Sa Hannu Kan Bukatar ABU Ta Koma Bakin Aiki.
✅Ministar Kudi Na Yin Zagon Kasa Ga Yaki Da Rashawa —Majalisa.
✅Ambaliyar Ruwan Bana Ta Fi Yi Wa Jigawa Barna Fiye Da Kowace Jiha – Minista
✅Muna bukatar karnuka domin yaki da 'yan kwaya a Najeriya - Marwa
✅EFFC ta kama tarin 'yan canji a Abuja da Lagos.
✅'Yan bindiga sun bukaci a biya Naira miliyan 30 kan ma'aikatan gona a Katsina.
✅Gwamnatin jihar Lagos ta kulle asibitoci 42 saboda rashin inganci.
✅Sama da 'yan gudun hijira 200,000 ne ke cikin yunwa a Najeriya - HRW.
✅Nijar ta bude makarantu a Ouallam bayan kullewar shekaru 5 saboda ta'addanci.
✅EU da AFD sun tallafawa Jamhuriyar Nijar a kokarin farfado da bangaren Ilimi.
✅Tawagar Gwamnatin Nijar ta ziyarci garin Tamou.
✅Muna neman wasu kasashe su taimaka wa bakin haure 234 da suka makale - SOS.
✅Sauyin yanayi na dakile kokarin kasashe wajen yakar illar da ya haifar- MDD.
✅UNESCO ta bukaci bin hakkin 'yan Jarida 208 da aka kashe daga 2020 zuwa 2021.
(c) Tauraruwa Hausa News.
www.tauraruwahausanews.blogspot.com
www.facebook.com/tauraruwahausanews
WhatsApp group👇🏼👇🏼
https://chat.whatsapp.com/CRb9IPKUBE0DE1oqMT88UV
Comments
Post a Comment