KIRA NA MUSAMMAN ZUWA GA MAIGIRMA GWAMNA
Daga Alhaji Bello Ibrahim (Alhajin APC)
GYARA KAYAN KA........
Assalamu Alaikum,
Bayan gaisuwa irin ta girmamawa zuwa ga Mai Daraja Gwamna.
Ya Maigirma Gwamna Hon Dr Bello Matawallen Maradun ina amfani da Wannan damar domin inyi kira akan bashin kuɗin Feeding na Makarantun Sakandare Wanda yanzu an tasarma Shekara ba'a biya ba, abunda ya gurgunta wasu Yan kasuwa sanadiyyar rashin biyan bashin, wasu sun gudu sunbar gidajen su akan wannan bashin, wasu kuma kasuwancin su ya tsaya cikkk duk akan wannan dalilin.
Maigirma Gwamna a Gwamnatocin da suka gabata ba haka aka gudanar da Wannan hulɗar ba.
Maigirma Gwamna Wallahi duk wanda bai faɗa maka cewa akwai illa Mai girma a cikin rashin biyan kudin nan ba to bai faɗa maka gaskiya ba, Wata kila ko ba masoyin ka bane, ko yana jin tsoron ka kasa fahimtar shi, ko kuma tsoron kada yabar samun abunda yake samu.
Maigirma Gwamna rashin biyan bashin nan ba daidai bane kuma yanada illa babba.
Maigirma Gwamna mutanen da ke da alaƙa da wannan bashin sun haura mutum ɗari biyar kuma duk sunada amfani ga Siyasa, sunada iyalai, Yan uwa da abokan arziki.
Maigirma Gwamna idan ma aikin ne baka iya cigaba da yin shi to a biya bashin baya Sai kowa yasan matsayin Shi.
GYARA KAYAN KA.
Comments
Post a Comment