ZAMAN GWANNONIN APC DA SHUGA BUHARI
Shugaban kasa Buhari ya shawarci a yi sasanci wajen zaben shugaban jam'iyyar APC na kasa
Gwamnoni kuma sun aminta da tsarin karba-karba na shugabancin jam'iyyar da ya dawo Arewa
A taron shugaban kasa Buhari da gwamnonin jam'iyyar APC, da ya gudana yau Talata, kan yadda za a gudanar da zaben sabbin shuwagabannin jam'iyyar a matakin kasa, shugaban kasa Buhari wanda shi ne jagoran taron, ya bayar da shawarar cewa, ba zabe yakamata a gudanar ba, game da shugaban jam'iyyar, kamata ya yi masu neman kujerar su zauna su sasanta kansu su bar wa mutum daya, saboda tabbatar da hadin kan junansu.
A taron kamar yadda Gwamnan jihar Kebbi ya bayyana wa manema labarai bayan kammala taron ya ce, shugaban kasa Buhari ya buga misali da cewa tun da aka kafa jam'iyyar APC ba a taba zaben shugaban jam'iyyar ba, sai dai a yi sasanci a bar wa mutum daya
"Bisi Akande shi ne shugaban jam'iyyar APC na farko, kuma an zabe shi ne ta hanyar sasanci, haka shima John Oyegun a zabe shi ne a ta hanyar sasanci, shi kansa Adams Oshiomhole an zabe shi a matsayi shugaban jam'iyyar APC ta hanyar sasanci" Inji shugaban kasa Buhari.
Shi ma a nasa bangaren lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i, ya bayyana cewa gwamnoni sun aminta da a dawo da rikon shugabancin jam'iyyar a shiyar Arewa, ganin shiyoyin kudu sun yi shekaru 8 suna rike da kujerar shugabancin jam'iyya
Comments
Post a Comment