INA MAKOMAR SIYASAR ABDULAZIZ YARI, MARAFA DA MABIYAN SU?
A satin da ya gabata ne daya daga cikin shugabanin "yan awaren APC reshen Jihar Zamfara wato tsohon Sanata Kabiru Garba Marafa ya kai ziyara a hedikwatar jam'iyyar APC ta kasa dake Abuja domin tantance katin shi na zama cikakken dan Jam'iyyar APC.
Isar sa ke da wuya ya tafi kai tsaye zuwa wurin rumbun adana bayanai na daukacin wadanda suka yi rejistar wannan jam'iyyar wato APC inda ya umurci mai bincike da ya bincika masa sunan shi ta hanyar lambobin katin rejistar shi.
Bayan kammala bincike kwakwaf da aka yi daga rumbun ajiyar, babu alamar suna ko lambar wannan rejistar shi ba a rumbun adana bayanai na wannan jam'iyyar. Rahotanni sun suna tsohon Sanatan ya fusata ya fita yana zage-zage.
Idan baku manta ba bayan sauya shekar da Gwaman Bello Matawalle yayi daga Jam'iyyar PDP zuwa Jam'iyyar APC hedikwatar Jam'iyyar ta bukaci kowa ya sabunta rijistar shi ta zama cikakken dan Jam'iyyar yayin da bangaren 'Yan awaren suka yi kememe suka ce ba zasu canza rejistar ba inda suka garzaya kotu.
A cikin watan da ya gabata hotuna sunyi ta yawo a yanar gizo na ganawar shugaban Yan awaren APC wato tsohon Gwamna Abdulaziz Yari tare da Bukola Saraki, Rabiu Musa Kwankwaso da kuma baya bayan nan tsohon mataumakin Shugaban Kasa wato Atiku Abubakar wadanda dukan su jiga -jigan jam'iyyar PDP ne.
Bayan sirri da muka samu sun nuna cewa ganawar sirrin da suka yi yana duba yiwuwar canza sheka ne zuwa PDP amma kuma a yanzu PDP tana hannun mutane biyu wato Gwamnan Jihar Ribas Nysom Wike da kuma Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.
A halin da ake ciki yanzu suna tunanin ya zasu kwace Jam'iyyar PDP daga hannun su ko kuma su dauki wata sabuwar Jamiyya.
Comments
Post a Comment