GWAMNAN JIHAR ZAMFARA YA KAI GAISUWAR TA'AZIYA A KARAMAR HUKUMAR ZURMI
Daga Muawiya Zurmi
Yau ne Midaraja Gwamnan Jihar Zamfara Hon (Dr) Bello Matawallen Maradun yayi ta'aziyar mutane 8 da ƴan bindiga sukayi garkuwa dasu a tsakiyar daminar da ta gaba ta kuma daga baya suka kashe su bayan kwashe tsawon wata takwas a hannun su
Gwamna yayi ta'aziyar ne ta hannun kwamiti mai karfi daya kafa domin suje suyi ta'aziya ga yan uwa da abokan arzikin wadanda suka rasa rayukan su kwamitin dai yana karkashin jagorancin Hon Abdullahi Muhammad Gurbin Bore Talban Zurmi da memmobinsa da suka hada da Shugaban Karamar Hukumar Mulki ta Zurmi Hon Dr Auwal Bawa Moriki, Mai ba Gwamna Shawara Hon Abubakar Justice Dauran da sauran muhimman mutane.
Comments
Post a Comment