AKWAI YIWUWAR SAUYA SHEKAR ABDULAZIZ YARI ZUWA PDP
Hasashe ya nuna tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma tsohon Dantakarar shugaban Jamiyyar APC ta Kasa zai iya sauya sheka daga jam'iyyar sa ta APC zuwa babbar jam'iyyar adawa ta kasa wato PDP.
Masu bibiyar al'amurran yau da kullum sun ce alkaluma sun nuna hakan bayan taron sirri da tsohon Gwamnan yayi tare da wasu jigajigan Jam'iyyar PDP a kwanakin nan.
Hotuna sunyi ta yawo a yanar gizo na taron sirrin da Yari yayi da Bukila Saraki, Rabi'u Musa Kwankaso tare da na baya-bayan su tsohon Mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar.
Wani bayanin sirri da Jaridar Taurarruwa ta samu ya bayyana cewa "A gaskiya Maigida (Yari) bai ji dadin bayyanar wadannan hotuna ba domin yayi taron a sirrance ne".
https://bazamfara.blogspot.com/2022/01/akwai-yiwuwar-abdulaziz-yari-ya-sauya.html
Comments
Post a Comment