DANSADAU: Jiya da Yau.

Daga Mohammed Kabir



 Dansadau gari ne da Allah Ya albarkata da abubuwa kala-kala. Daga girman kasa zuwa yawan jama'a, albarkatun kasa, filin noma da kiyo da sauran abubuwan habaka tattalin arziki.

A kimanin shekaru 15 zuwa 20 da suka gabata a duk fadin jihar Zamfara babu yankin da aka yi itifakin ya ke samun cigaba kamar wannan yanki, sai dai kash! yanzu labari ya canza kasancewar halin da kasar ta samu kanta na mummunar matsalar tsaro a cikin kusan shekaru goma da suka wuce.


A halin da ake yanzu yawan hare- haren da ake kawo ma wannan garin yayi sanadin mutane da yawa suna gudun hijira daga garin zuwa wasu garuruwan domin tsira da rayukan su.


Daga watan Janairu na wannan shekarar zuwa watan 7 anyi garkuwa da mutane fiye da 500 a wannan yanki, wasu matafiya wasu kuma mazauna garin inda aka kashe mutane da yawan su.


A cikin watan da ya gabata, a kauyen Kabaro da yake cikin gundumar Dansadau 'Yan ta'adda suka harbo jirgin saman yaki na sojojin Najeriya wanda wannan ba karamin abun mamaki bane ga wadanda basu da masaniya akan tarin miyagun makaman da wadannan 'Yan ta'adda suka tara kamar yadda rahotanni suke zuwa daga mazauna kauyuka.



Duk a cikin watan Yan bindigar suka kawo wani hari a cikin garin Dansadau inda suka kashe mutum 4 kuma sukayi garkuwa da wasu da dama. Bayan sati daya da wannan hari suka kawo wani harin na samame a Babbar asibitin garin inda suka dauke wani hadimin  asibiti da wani mutum daya mai jinya bayan sunyi yunkurin garkuwa da likitocin asibitin wanda basu samu nasara ba.


A halin da ake ciki yanzu hanyar da ta hada Dansadau da Gusau ba mai iya bin ta ba tare da rakiyar Jami'an tsaro ba. Motoci sukan yi kwana da kwanaki suna jira har lokacin da aka samu jami'an tsaron da zasu masu rakiya shiga ko fita garin. Akan samu motoci daga 20 zuwa sama masu jiran a masu rakiya.


Akan samu tsinkewar kayan masarufi da suka hada da Gishiri, Magi, kayan miya da sauran su a sakamakon tsoro da 'Yan kasuwa da kuma Direbobi suke ji na bin hanyar.


Ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jiha da suyi iya kokarin su na sauke nauyin da Allah Ya aza masu domin mutanen wannan yanki suna cikin halin kunci da mummunan yanayi.


Muna rokon Allah Ya kawo muna zaman lafiya a wannan Jiha tamu da kasa baki daya, Amin.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA