SABON SHUGABAN HUKUMAR KULA DA MA'AIKATAN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YA KAMA AIKI





Yau Laraba 16 ga watan Disamba 2020, Sabon Shugaban Hukumar kula da Ma'aikatan Majalisar dokokin Jihar Zamfara wato Hon. Mansur A. Musa Bungudu ya kama aiki a ofishin sa dake rukununin gidajen Kwamishinoni dake hanyar bypass a garin Gusau.


Shugaban hukumar Hon. Mansur Bungudu ya samu tarbo daga ilahirin Ma'aikatan hukumar wanda Sakataren hukumar Alh Chika Isiya ya jagoranta. Da yake bayani bayan gabatar da Ma'aikatan hukumar, Alhaji Chika Isiya ya bayyana halayen sabon shugaban hukumar masu kyau da nagarta kasancewar sunyi aiki tare a tsawon shekaru 8 lokacin yana Dan majalisar Jiha mai wakiltar Bungudu ta Yamma.


Da yake bayani sabon shugaban hukumar, Hon. Mansur Bungudu ya yi godiya tare da neman hadin kan daukacin Ma'aikatan domin ganin Gwamnan Jihar Zamfara Dr. Bello Muhammad Matawallen Maradun ya samu nasara a tsawon mulkin shi.


Sabon shugaban ya samu rakiyar Hon. Abdullahi Muhammad Dansadau, Hon. Salisu Kainuwa Tsafe, Hon. Abubakar Ajiya, Hon. Aminu Abubakar D/Jibga tare da Hon. Hashimu Shehu Gazura wanda shine Kwamishinan Dindindin a hukumar Zabe ta Jihar Zamfara.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA