GWMANAN JIHAR ZAMFARA YA NADA SHUGABAN HUKUMAR MA'AIKATAN MAJALISAR DOKOKI TARE DA KWAMISHINAN DINDINDIN NA HUKUMAR ZABEN JIHAR.
A ranar talatar da ta gabata ne Gwamnan Jihar Zamfara Hon. DR. Bello Muhammad Matawalle ya mika takardar kama aiki zuwa ga Hon. Mansur Ahmad Musa tsohon Dan majalisar Jihar Zamfara mai wakiltar Bungudu ta Gabas a matsayin shugaban Hukumar Ma'aikatan Majalisar dokoki ta Jihar Zamfara.
Da yake bayani bayan karbar takardar kama aiki, Hon. Mansur Ahmad yayi godiya ga Maidaraja Gwmana tare da bashi tabbacin aiki tukuru wajen ganin an samu nasara a lokacin tsawon mulkin shi tare da bashi goyon baya ta kowa ne hauji.
A dayan bangaren Hon Hashimu Shehu Gazura ne ya karbi takardar kama aiki a matsayin Kwamishinan Dindindin a Hukumar zabe ta Jihar Zamfara. Hon Gazura ya yi godiya ga Maidaraja Gwamna na damar da ya bashi domin yima jama'ar Jihar Zamfara aiki haka kuma ya nuna cikakken goyon bashi wajen ganin wannan gwamnati ta samu nasara.
A cikin tawagar da suka yi wa sababbin masu mukamai sun hadu da Hon. Abdullahi Muhammad Dansadau wanda shima tsohon Dan majalisar dokoki na Jihar Zamfara wanda ya wakilci Maru ta kudu, Hon Dayyabu Adam Rijiya tare da Hon. Vita Nasrawa.
Comments
Post a Comment