SHUGABA BUHARI DA HAUSAWA
Daga Muhammad Bin Ibrahim
Zuwa yanzu, abin da ke bayyana a tsakanin Hausawa, al'ummar da ta nuna qulafucin so ga Shugaba Muhammadu Buhari fiye da yadda ta nuna wa kowane mahaluki a duniya, shi ne nadama. Nadama a kan zaben tumun daren da suka yi. Saboda sun farga cewa abin da suka tsammana a tattare da shi ba haka ba ne. Yanayin nadama mummuna ne, don haka wanda ya samu kansa a ciki abin tausayi ne koda kuwa da gangan ya sa kansa tun a tashin fari.
Sai dai kuma, kamar yadda kowane yanayi mai kyau yake da bangarensa mara kyau, haka ma kowane yanayi mara kyau yake da bangare mai kyau. Halin da mu Hausawa muke ciki a yau game da batun shugabanci, hali ne mara kyau da dadi, don mun fi sauran al'ummomin qasar fuskantar uquba, amma kuma halin yana tattare da guzirin busharar farin ciki a gare mu in har muka yarda muka amfana da yanayin ta hanyar tsara lamurranmu da kyau.
Yanzu mun gane cewa, gaskiyar mutum ko da'awar gaskiyarsa, ba su ne kadai ababen buqata ga shugaba mai kamantawa ba. Yanzu mun gane cewa farfagandar dan takara kan ayyukan da zai yi, ba ita ce kadai mizanin auna shi ba. Yanzu mun gane cewa zaman shugaba dan bangarenmu ko dan addininmu, ba su ne hujjar tabbatarsa nagari a shugabanci ba.
Ba za a iya tababa ba, idan aka ce, da a ce Buhari bai zama shugaban qasa ba, da ba za mu gane wannnan karatu ba. Saboda ba karatun da ake koyo a aji ba ne, karatu ne na tajriba (experience), yanayi ke sa al'umma ta gane. Muna godiya ga Allah kan wannan ilimi duk da muna shan wuyarsa.
Amma ba iya nan za mu tsaya ba, mene ne abin yi? Wa yakamata mu zaba a shekarar 2023? Mene ne darajojinsa? Wane shiri za mu fara tun yanzu?
Amsar nan ba ta mutum daya ba ce, tamu ce duka. Ina mufakkiranmu? Don Allah su zo su zaqulo mana yadda za mu yi.
Comments
Post a Comment