AREWA MU FARKA
Daga Muhammad Abba.
1. Akwai son zuciya da kin aminta da gaskiya indai har ba daga bakin ka ko naka ta fito ba.
2. A matsayin mu na musulmai muna danganta komai da addini, muna wuce iyaka, shiyasa malamai yan Scope suke wasa da hankulan mu.
3. Har yanzu mun kasa gane cewa democradiya ba addini bace, shiyasa yan Arewa ke yakan kawunan su lokacin siyasa.
4. Shuwagabannin Arewa basu damu da talaka ba, abinda ya dame su shine aljihunan su.
5. Masarautu sun koma mabarata, maroka kuma yan maula shiyasa basu fada aji, domin a Arewa ne kadai dan siyasa ke wasa da masarauta yanda yake so, Chairman ma sai ya tumbuke sarki ya zauna lafiya, a kudu kuwa karyan shugaban kasa ya raina masarautar da tafi ko wacce kankanta.
6. A arewa siyasa ta kan makantar da mutum, shiyasa ko ana kashe makwabcin sa, indai har bata shafe shi ba, bazai fito ya kalubalanci hakan ba, har sai kaga wani yana yabon shugaba da ke ci sobida yana amfana da jam'iya ko soyayya marar amfani.
Da dai sauran su.
Idan dan arewa bai bambanta addini da siyasa ba, ko kuma cigaban kasa da son zuciya ba, arewa babu inda zata dosa, kuma kaman yanzu aka fara.
Idan musulmai da kristan arewa bazasu gane cewa idan siyasa tazo maganganun mafi yawancin malaman addini karya ce da son zuciya ba, toh fa lallai babu inda arewa zata je.
Mafi amfani shine, idan babu soyayyar kasa fiye da soyayyar zuciya, siyasa ko wani bangarenci ba, arewa murkushewa zata yi ta yi.
Ina fadan hakan ba don bana son Arewa ba, ko kuma nafi son Kudu fiye da Arewa ba, ni dan Najeriya ne, inason cigaban kasa gabaki daya, amma kashe kashe da akeyi a Arewa yayi yawa, a ko wace sa'a sai an kashe bayin Allaah, amma har wa yau mutane suna son zuciya basa tunani.
Casinos & Slots | DRMCD
ReplyDeleteThere's 공주 출장마사지 also a casino that is also offering live dealer games for your 공주 출장마사지 table games. Casino-Online 강원도 출장마사지 Gambling FAQs. casino and online 양산 출장안마 casino 안산 출장마사지 software,