A SHIRYE MUKE MU YAKI DUK DAN KUDUN DA YA KE SON KIFAR DA GWAMNATIN BUHARI TA AMFANI DA ZANGA-ZANGAR ENDSARS

 


Shettima Yerima


Shugaban kungiyar matasan Arewa, Yerima Shettima, yace 'yan Arewa baza su rike hannuwan su suna kallon 'yan Kudu su tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari akan mulkin Najeriya ba.


Da yake zantawa da 'yan jaridu a Minna babban birnin jihar Neja, Shettima ya ce 'yan Kudu suna neman su kara cutar da 'yan  Arewa kamar yadda suka yi bayan mutuwar Umaru Musa Yar'Adua. 


Ya kuma bayyana shirin 'yan Arewa dangane da fitowa yaki idan har masu zanga-zangar sun bukaci shugaba Buhari ya sauka ko kuma su kawo karshen kasar Najeriya.


"Tun daga shekarar 1999, 'yan kudancin Najeriya suke cutar da mu game da abinda ya shafi kujerar shugaban kasar Najeriya"


"A lokacin da Obasanjo yake shugabancin Najeriya babu wani dan Arewa da ya takura masa har sai da ya kammala wa'adin mulkin sa na shekara 8 a ofis."


"Dan uwan mu Yar'Adua yana hawa mulkin Najeriya suka fara sukar gwamnatin sa har sai da ya mutu, a maimakon a dauki wani dan Arewan ya karasa wa'adin mulkin Yar'Adua sai suka cuso mana Jonathan" A cewar Shettima


Ya kuma kara da cewa "Yanzu kuma dan uwan mu Muhammadu Buhari ya sake hawa kan karagar mulkin Najeriya, suna amfani da duk wasu hanyoyin yakar sa, sun manta cewa har yanzu muna da sauran wasu shekaru 8 bayan wa'adin mulkin Buhari wadanda sune zasu zama makwafin shekarun da Jonathan da Obasanjo suka yi a mulkin Najeriya"


"Abin lura a nan shine mu 'yan Arewa baza mu aminta da wannan abinda suke yi ba. Gaba dayan mu zamu fito yaki idan masu zanga-zangar ENDSARS suka nemi Buhari ya sauka ko kuma suka nemi a kawo karshen Najeriya kamar yadda wasu suke yi a jihar Anambra" Inji shi.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA