LABARI DA DUMI-DUMI: TSOFAFFIN YANMAJALISU DA KWAMISHINONI ZASU KOMA JAM'IYYAR PDP.
Wasu daga cikin tsofaffin Kwamishinoni da Yan Majalisun jihar Zamfara zasu canza sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP.
Adadin Yan majalisa 9 da Kwamishina 6 ne suka nuna ra'ayin canza sheka daga APC zuwa PDP bayan wani taron sirri da akayi dasu a garin Kaduna.
Da yake bayani bayan kammala taron, Sakataren kungiyar da ya bukaci a boye sunan shi yace sun yanke wannan shawara ne domin sun aminta da salon mulkin Gwamna Bello Matawalle.
Comments
Post a Comment