DAN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA MAI WAKILTAR MARU TA AREWA YA RABA KAYAN TALLAFI GA MAZABUN SA



Yau Alhamis, 23 ga wayan Afirilu Dan Majalisar dokokin Jihar Zamfara mai wakiltar Maru ta Arewa wato Hon. Yusuf Alhassan Kanoma ya raba kayan tallafi ga jama'ar da yake wakilta.

Tallafin da ya hada da Baburan hawa tare da injimin nika da sauran abubuwa domin rage radadin talauci ga jama'ar da yake wakilta.

Da yake bayani tayin bada tallafin, Hon. Yusuf Kanoma yayi kira ga jama'ar da suka magana da suyi amfani da wadannan tallafi da suyi amfani dashi ta hanyar da ya kamata.


Game da yanayi da ake ciki na annobar Coronavirus, yayi kira ga jama'a da suyi shawarwarin da likitoci suka bada akan kariya wajen kamuwa da wannan cutar.

Da yake bayani, daya daga cikin wadanda suka amfana da wannan tallafi ya yi godiya ga Hon. Kanoma tare da addua Allah yayi mashi jagoranci ya kuma taimake shi ya gama mulkin lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA