CUTAR CORONAVIRUS: INA MAFITA GA TALAKAN NAJERIYA?


Daga Dr. Hakeem Baba-Ahmed



    Mutane da yawa na ganin ba dole ne su bi ka’idojin da hukumomi  ke shimfidawa ba, da shawarwarin  jami’an lafiya suke bayarwa wajen kare kai daga Coronavirus, musanmam ma zama a gida, nesa da juna da wanke hannaye ba. Mafi yawan jama’a suna cewa hujjar su ita ce basu da abin da zasu biya bukatun su muhimmai idan basu fita ba, har ma da gwamutsuwar da jama’a ke yi. Wadannan hujjoji karfafa ne, kuma ya zama dole ne hukomomi   su tashi su taimaki jama’a musanman da abin da zasu ci idan sun zauna a gida har na wani tsawon lokaci kamar makonni.

      Wadansu kuma gani suke ‘yancin su ne su dauki dokar da suke so, su kuma yi watsi da wadda basu so, koda kuwa suna iya bin dokokin.Wasu na kawo siyasa da hujjojin bukatar yin ibada wajen biris da dokokin tsare kai.Wasu da yawa kuma hujjar su ita ce sun gaji da zaman gida, saboda haka zasu rika fita fira ko su fita yawo inda zasu hadu da sauran mutane.

         Wallahi Tallahi wannan ciwon na corona virus ba karya ba ce, kuma babu ruwanta da arzikin ka, ko talaucin ka, ko siyasar ka, ko addinin ka. Idan mutum yace zai ki bin dokokin tsare kansa da iyalin sa da sauran jama’a, ba illa yayi wa gwamnati ba, kansa ya yi wa. Komi talaucin ka, Allah vai dauke maka nauyin taimakon kan ka da tsare kanka ba. Shugabanni da sauran manya da muke gani sun ki taimaka mana suna iya kare kansu, su bar mu, ga talauci ga ciwon corona virus.

        Komin kokarin mutane a cikin wannan hali da muke ciki, dole ne sai gwamnatoci sun taimaka wa jama’a wajen bin ka’idojin tsare kan mu. Kuma idan da gaske suke yi, kuma suna so su taimaka, gwamnatocin tarayya da na jihohi suna iya taimakawa mutane mara shi, su zauna a gida a basu abin da zasu fita su nema.Idan hukuma ba zasu taimaka ba, jama’a kuma ba zasu iya zama a gida su bi dokokin tsare kai daga wannan cutar ba, a gaskiya mun shiga uku.Wannan ciwon zai zama mana tsumangiyar kan hanya.

       Allah Ya tsare mu da tsarewar Sa, Ya kuma bamu ikon yin abin da Ya ce,”Tashi In taimake ka”.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA