SOJA WANDA YAYI SHAHADA A DANBUWA
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
Yau kenan yayinda yan ta'addan boko haram sukayi barin wuta da sojojin mu na Nigeria a Danbuwa, jihar Borno. Wannan bawan Allah da kuke gani sunan sa Haruna. Dan jihar Taraba ne, daga karamar hukuman Jalingo. Yana daya daga cikin wadanda sukayi shahada a yau a filin daga.
Ya mutu saboda kasarsa ta zauna lafiya.Ya sadaukar da rayuwansa saboda kare al'umman kasarsa.Ya bada rayuwansa saboda kare mutanen kasarsa Nigeria
Ya Allah kayi masa Rahama ka karbi shahadarsa kasa aljanna ce makomarsa. Amin summa amin.
Marubuci: Aminu Suleiman Jawar.
To Allah ya taimaka
ReplyDeleteTo Allah ya taimaka
ReplyDelete