KIWON LAFIYA: CUTAR SANKARA KO DAJI
Daga Aliyu Samba.
Cutar sankara ko cancer da turanci na daya daga cikin cututtukan da ke adabar al’umma a wannan zamani, kuma cuta ce da take da matukar wuyar sha’ani.
Cutar Sankara Babbar matsala ce a cikin al’umma saboda yawan kawo jinya da rashe-rashen rayuka da take yi. Wasu ana iya kare kai daga kamuwa da su, wasu kuma sam haka nan kawai suke kama mutum, musamman idan yana dauke da nakasa a cikin kwayoyin halittunsa na gado.
Cutar ta sankara tana da nau’o’i daban-daban saboda tana kama sassa daban-daban na jikin mutum. Ga manya daga cikin sassan jiki da cutar ta fi kamawa a wannan kasa tamu.
A) MAZA:
1- Sankarar halittar Prostate Gland.
2- Sankarar Hanta.
3- Sankarar kwayoyin Jini.
4- Sankarar Hanji
B) MATA:
1- Sankarar Nono
2- Sankarar Bakin Mahaifa.
3- Sankarar kwayoyin halittu na obary (kwan mace).
4- Sankarar Hanji.
C) YARA:
1- Sankarar Kumatu.
2- Sankarar kwayoyin Jini.
3- Sankarar Ido.
4- Sankarar kashi
A Najeriya dai an fi samun cancer ta mahaifa (Cervical Cancer) da ta mama (Breast Cancer) ga mata, da kuma ta mafitsara (Prostate Cancer) ga maza.
Me ke jawo Cutar Sankara
Masana dai sun ce babu wani takamaiman abu da za a ce shi ke jawo cancer, amma akwai abubuwan da ke sanadinta. Wadannan sun hada da
1- Yawan shekaru
2- Yawan kiba
3- Yawan zubar da ciki sai 4- Yawan haihuwa ba tare da tazara tsakani ba
5- Shan Giya (Alcohol)
6- Shan Sigari (Smoking)
Da dai sauransu.
Yanda Sankara ke faruwa
kwayoyin halittu na jikinmu, wadanda suka hadu suka yi sassa daban-daban a jikinmu kamar hanta da huhu da zuciya, da ake kira cells suna rayuwa ta ’yan kwanaki, su kuma hayayyafi wasu sababbi kafin su mutu. Idan ciwon sankara zai faru, wadannan kwayoyin halittun maimakon su mutu idan lokaci ya yi, sai su rikice su ki mutuwa, su yi ta hayayyafa ba qaqqautawa.
Alamomin Cutar Sankara
Da yake kwayoyin halittun da ake ta hayayyafa ba kakkautawa su ma abinci suke ci, cikin sauri sukan cinye dan abin da aka ci, nan da nan za a ga mutum ya zabge saboda rashin isasshen abinci. Banda rama kuma, sauran alamun da ake gani a fara tunanin ko mutum ya kamu da ciwon daji sune:
1- Yawan kasala saboda rashin abinci da rashin jini a jiki.
2- Rashin jin dadin abinci a baki.
3- Wani lokaci akwai fitowar kari ko rami a wurin da kansar take.
4- Sai jin zafi a wurin a wasu lokuta.
5- Idan a kashi ciwon ya fito za a iya samun karaya.
Da sauran dai alamomi wadanda kowace kansa ke da ita daban.
Matakan magance cancer
Akwai matakai uku da ake bi don magance wannan cuta ta cancer.
1- bayar da magani na hadiya ko allura. (Drugs)
2- Tiyata (Surgery)
2- Kona wajen tsiron cutar (Chemotherapy)
Amma duk hanyoyi ukun suna yi wa mutane da dama wahala saboda rashin walwalar aljihu.
Hanyoyin Kariya
Abin da masana suka gano, wadanda idan aka kiyaye za su iya kare mu daga sharrin cututtukan Sankara sun hada da:
1- Barin amfani da taba sigari, wadda ban da sankarar huhu takan iya kawo sankarar tantanin fitsari da na hanji da ta makogaro.
2- Barin amfani da ruwan barasa, wato giya, wanda kan iya jawo sankarar hanta, hanji, huhu, koda da Nono.
3- Daina yawon banza ga mata. An yi amanna ciwon kansa na bakin mahaifa ya fi kama mata masu zaman kansu da mata masu yawan auri-saki, saboda su suka fi hadarin kamuwa da kwayar cutar Virus ta human papilloma, mai sa kansar bakin mahaifa.
4- Alluran rigakafi kan taimaka wajen kiyaye wasu nau’i na Sankara. Akan iya kiyaye kamuwa daga Sankarar hanta wadda kwayar cutar birus ta hepatitis rukunin B. ke kawowa idan aka yi wa mutum allurar Rigakafin ta. Duka ma’aikatan lafiya wadanda su ne suka fi shiga hadarin kamuwa, akan so su karbe ta. Sai kuma jariran da mahaifansu ke dauke da kwayar cutar hepatitis din, su ma yana da kyau da zarar an haife su a kai su a yi musu. A yanzu ana samun wannan allura a asibitocinmu kuma an sa ta a jadawalin alluran riga-kafi na kasa baki daya, ta yadda kusan duk jaririn da aka haifa aka kai allura, sai an yi masa.
5- Kiyaye yara daga yawan cizon sauro. An tabbatar da cewa ciwon Sankarar kumatu (Burkitt lymphoma) a yara yana daya daga cikin cututtukan da yawan cizon sauro ke kawowa. Don haka yawan sa yara cikin gidan sauro da dare zai taimaka matuka gaya.
6- Sai yawan rage shiga rana wanda kan iya kiyaye Sankara ta fata, musamman a mutane masu hasken fata.
7- Rage kiba. Masana sun tabbatar da cewa masu kiba sosai suna cikin hadarin kamuwa da ciwon sankara, musamman idan wani a danginsu ya taba yin ciwon. Don haka sai a rage maiko a abinci, a rika kara ganyayyaki da kayan itatuwa. Sai kuma a hada da yawan motsa jiki
8- Binciken masana a duka sassan duniya ya tabbatar da cewa yawan shan koren shayi wato green tea kan iya rage hadarin kamuwa da ciwon dajin kowane sashe na jiki, domin shi koren ganyen yana da sinadarai masu yawon neman irin wadannan kwayoyin da suka bijire suke zama kansa kuma su yi maganinsu.
9- Duk wadanda suka ba shekaru hamsin baya kuma maza ne ko mata, yana da kyau duk bayan shekaru biyu-biyu su rika zuwa tantance cututtukan daji na hanji ta hanyar gwajin bayan gida, wanda yanzu akwai a asibitoci musamman na kudi. Mata kuma da suka haura hamsin yana da kyau su rika zuwa awon tantance cututtukan daji na mama da na bakin mahaifa. Duka wannan ya zama wajibi ga wadanda za su iya domin idan aka gano daji da wuri, an fi iya maganinsa. Idan aka gano ciwon daji a kurarren lokaci, maganinsa sai an sha wahala.
Comments
Post a Comment