INA MAKOMAR TSARON NAJERIYA?



Daga Datti Assalafiy


Majalisar Dattawa da sauran al'ummar Kasa suna cigaba da yin kira ga Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya akan ya tsige manyan hafsoshin tsaron Nigeria, tare da maye gurbinsu da sabbi

A nazari da tunanin masu wannan kiran ga shugaba Buhari shine cews idan ya aiwatar da bukatarsu hakan zai zama sanadin magance matsalar tsaron Nigeria a halin da ake ciki

To amma ga mutanen da suka san sirrin tsaron Nigeria zasu tabbatar muku da cewa tsige shugabannin tsaro da maye gurbinsu da wasu sabbi ba zai canza komai ba, ko da za' samu canji na lokaci ne kankani lamarin tsaron Kasar zai cigaba da tafiya a yadda yake

Amma ina ne matsalar tsaron Nigeria yake? kuma ta ina za'a magance matsalolin tsaron? Ku daure ku karanta wadannan mas'alolin tsaron Nigeria guda sha-shida (16) wanda ni Datti Assalafiy dalibin jami'ah dake karatu a fannin kimiyyar Laifuka da Tsaro na wallafa kamar haka:
!
(1) Duk wanda ke son fahimtar wannan sai yayi tunanin abinda yasa mutanen da aka basu amana a bangaren jagorancin tsaro suke cin amanar da aka basu tare da danne hakkin na kasa da su

(2) Sai an fahimci dalilin da yasa jami'in tsaro yake karban na goro a hannun direban motocin fasinja

(3) Sai an fahimci dalilin da yasa jami'in tsaro yake karban kudin beli a hannun fararen hula, da kudin da zai sayi takardan da zai rubutu jawabin mai kara da wanda ake kara da shaidu, idan bai karbi kudin sayan takardan ba sai dai yacire a aljihunshi ya saya

(4) Sai an fahimci dalilin da yasa za'a kawo ma jami'an tsaro korafi ana bukatar su hau motarsu don kai agajin gaggawa, amma sai suce babu kudin mai, kuma da gaske babu kudin man!

(5) Sai an fahimci dalilin da yasa wasu gurbatattun jami'an tsaro kan hada baki da miyagun mutane masu cutar da zaman lafiyar al'ummah suna karban cin hanci daga garesu

(6) Sai an fahimci dalilin da yasa wasu gurbatattun jami'an tsaro kan karbi toshiyar baki daga gurin dillalen miyagun kwayoyi da manyan dilolin tabar wiwi

(7) Sai an fahimci dalilin da yasa manyan ofisoshin jami'an tsaro ke kashe kudin aljihunsu wajen neman hanyar da za'a kaisu Maiduguri yaki da Boko Haram saboda danne hakkin na kasa da su

(8) Sai an fahimci dalilin da yasa lauyoyi masu zaman kansu suke jiran 'yan sanda su gabatar da wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a kotu don su tsaya masa su samu makudan kudi su kubutar dashi

(9) Sai an fahimci ta ina ake shigowa 'yan ta'addan Boko Haram da masu garkuwa da mutane manyan makamai masu hatsari?

(10) Sai an fahimci ta ina ne ake kawo ma 'yan Boko Haram da masu garkuwa da mutane man fetur da gas har cikin jeji, wanda suke zubawa a motoci da babura su hau su shiga garin mutane suyi ta'addanci

(11) Sai an fahimci hanyar da ake kawo ma 'yan Boko Haram da masu garkuwa da mutane magunguna da miyagun kwayoyi

(12) Sai an fahimci dalilin da yasa kungiyoyin turawa na sharri wai kungiyoyin agaji wanda ba na gwamnati ba ( International NGOs) da suka mamaye Kasar Borno da Yobe suna taimakon 'yan Boko Haram ta karkashin kasa

(13) Kuma sai an fahimci dalilin da yasa ake cin amanar jami'an tsaron da suka sadaukar da rayuwarsu domin Nigeria ta zauna lafiya

(14) Sai an fahimci dalilin da yasa ake cin amanar fararen hula masu bayar da sahihin rahoto akan bayanan sirrin tsaro

(15) Sai an fahimci dalilin da yasa 'yan jaridu ke samun bayanan sirrin tsaro fiye da hukumomin tsaron dake dauke da alhakkin kula da tattara bayanan sirrin tsaro

(16) Sai an fahimci dalilin da yasa jami'an tsaro da sukayi yaki suka kare Kasa, suka sadaukar da rayuwarsu, bayan sunyi ritaya daga aiki suke shan wahala kafin a biyasu kudinsu na giratuti, wa su kuma suke sake komawa aikin gadi maimakon su huta tunda sun tsufa

Idan majalisar Dattawa da sauran masu ruwa da tsaki a Kasar suka taimaki gwamnatin shugaba Buhari ta magance wadannan matsaloli guda 16 da Datti Assalafiy ya bayyana, to za'a samu mafita mai dorewa game da tabbatar da tsaron Nigeria

Ban wallafa wannan rubutun don bayyana gazawar wani ko kuma yiwa wani batanci ba, gaskiyar lamari na bayyana saboda kishin kasa, don haka ayi hakuri.

Ina rokon Allah Ya yiwa shugabannin Nigeria jagoranci, Ya basu ikon aikata abinda yake alheri ga zaman lafiyar Nigeria Amin.

Za'a iya tuntubar marubuci ta Gmail: Dattiassalafiy@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA