ILLOLIN SHAYE SHAYEN MAGUNGUNAN DA MUKE BA BISA KA'IDA BA
Daga Dr. Kabir Yusuf.
Shayen shayen magungunan da muke a gidaje da zaran munji zazzabi ko ciwon kai na daya daga cikin dalilan dake sa ana samun mafi yawan cutukan Hanta a wannan lokaci da muke ciki.
Dabi'ar jika ma yaranmu kanana kwayoyin paracetamol na gaba gaba wajen haifar da matsala tin muna Yara daga karshe matsalar ta bijiro lokacin da girma yazo mana.
Illolin magungunan da muke dauka ba wani abu ba ko muke ganin basa iya haifar mana da komai sune gaba gaba wajen haifar da dinbin matsalolin da muke samu yanzu musamman anfani da kwayar paracetamol da magunguna na antibiotics ga matanmu.
Kwayar paracetamol daya tana zuwa da nauyin 500mg Wanda sai yaro yakai shekara 14 sannan zai iya daukan kwaya 2 na paracetamol shine muke jika ma Yara Yan kasa da shekara 5 wani Abun bakinciki hadda ire-iren masu Kari dinnan Wanda suke zuwa extra wani magani daban kamar Sudrex, Boska da sauran su.
Muyi ma kanmu kiyamullaili muguji jefa diyanmu cikin matsala da yanayi tin kafin girmansu yazo. Da kanmu muke jawowa kanmu asarar kudade lokacin da matsaloli suka bijiro sanadiyar bayarda ire iren wadannan magungunan masu HYPERSENSITIVE REACTION ga diyanmu Wanda basuda karfin garkuwar jiki.
Ya Allah ka wadata mu, ka cire Mana kyamar zuwa asibiti da zaran mun fara zazzabi, ya Allah ka fahimtar damu magidanta anfanin zuwa asibiti dan kaucewa ire iren wadannan matsalolin Amen.
Comments
Post a Comment