Ministan Yan Sanda Dingyadi da Sanata Wamakko da Tsohon Gwamna Yari na kitsa shirin haddasa rashin tsaro a Zamfara.
Daga Shafin Maniyarzamfara.com
Tsohon gwamna Abdul'aziz Yari Abubakar a ran Larba ta wannan makon yayi wani taron sirri da Ministan Yan Sanda kasa Muhammadu Maigari Dingyadi tare da shugaban kwamitin tsaro Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a gidan Wamakko dake Asokoro, garin Abuja tare da manufar zargin da akeyi na neman a dauke Kwamishinan Yan Sanda na Jihar Zamfara Muhammadu Dangogo.
Bayanin wata majiyar ta baiyana taron na sirri da aka mayar da sunan ziyara ga tsohon gwamna Wamakko yana da manufar hargitsa zaman lafiya na jihar Zamfara don cimma burinsu ga samun iko a matakin tsaro.
Anji cewar tsohon gwamna Yari ya yiwa Ministan alkawalin tallafi da samar masa da wasu makudan kudade akan ya tabbatar da Sufeton Yan Sanda yabi umurninsa don dauke kwamishinan Yan Sanda tare da kawo nasu dake yanzu haka a hedikwatar Yan Sanda ta kasa bayan karin girman da akayi masa.
Sanata Wamakko shine Shugaban kwamitin tsaro na Majalisar Dattawa yayin da ake zargin yana da hannu akan kusan wata barazanar da EFCC ke yiwa wasu manyan jami'an gwamnatocin jihohin Sokoto da Zamfara akan basu tsoro da neman tsare su akan zargin karya da na bogi na cin kudaden gwamnati.
Duk da yake EFCC ta kasa hukunta Yari da Wamakko akan zargin lamushe makudan kudaden baitulmalin jihohinsu, har yanzu ana ganin kamar suna da daurin gindi daga wasu manyan jami'an gwamnatin tarayya dake da kusanci da fadar shugaban kasa.
Yanzu haka dai tsohon gwamna Yari na bin duk hanyoyin da yake iyawa wajen haddasa rudani da dawo da hare - haren ta'addanci da satar jama'a abin da yayi sauki fiye da watanni biyar da suka gabata.
Zuwa yanzu dai wani kwamiti na Majalisar Dattawa ya aika takardar gayyata don neman zuwan Kwamishinan Yan Sanda na jihar Zamfara a gabansa da nufin amsa wasu tambayoyin da ake ganin neman bata masa suna don dauke shi daga jihar ta Zamfara.
Daga
Manuniyarzamani.com
Comments
Post a Comment