GINA JAMI'A MALLAKAR GWAMNATIN JIHAR ZAMFARA, YA ABUN YAKE TUN FARKO?




Daga Alhajin APC



 BAKI MAI YANKE WUYA.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya tabbatarma duniya da cewa Gina jami'a a Zamfara bashida Wani
Muhimmanci, a wata dogowar fira da a kayi da shi a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna a 2012.

"Jami'a ba itace Matsalar Jihar Zamfara Ba, Inji Abdulaziz Yari"

Hujjojin da Audu Yari ya bayar na rashin Muhimmancin Gina Jami'a a jihar Zamfara sune:

✅Jihar Zamfara titi ne matsalar su ba gina Jami'a ba.

✅Hujjar Shi ta biyu itace Wai daliban jihar Zamfara baza su amfana da Jami'ar ba idan an gina ta, kasancewar basa cika gurabin su a Jami'o'in da muke Makwabtaka da su kamar Usmanu Danfodiyo University, B.U.K, ABU, F.U.K (Dutsin ma) da Makamantan su.

Lokacinda Audu Yari ke wannan hirar rankatakaf din Najeriya jihar muce batada irin wannan jami'ar, a haka Audu Yari ya kafe kafafuwan Shi cewa lallai baza'ayi Jami'a ba, Allah Manyasha'u Sai Ya Kaddari Tsohon Shugaban Kasa Good luck Jonathan ya bada umurnin kirkirar Sabbin jami'o'i ciki harda Zamfara.

Samun Jami'a Mallakar Gwamnatin tarayya a Gusau baiyima Audu Yari dadi ba, Saboda Gudumuwar da aka nemi Ya bayar don ganin wannan jami'ar ta tafi yadda ake bukatar ta tafi bai bayarba har Allah Ya karshen wa'adin Mulkinshi na Mutakabbirinci da hassadar Karatun diyan Talakawa.

WADANNE DALILAI NE SUKA SANYA AUDU YARI SAKEYIN TUNANIN GINA JAMI'A MALLAKAR JIHA?

✅ Dalili na farko Shine Jari hujja, idan baku manta ba munce a hirar da yayi da Gidan Rediyon tarayya na Kaduna yace yin aikin Titi yafi Muhimmanci, kuma kowa yasan akwai Percentage Mai nauyi ga aikin titi, domin babu aikin da yafi titi tsadar yi a Gwamnatance, irin wannan dalilin yasa da yaga Wa'adin Gwamnatin Shi ya kawo karshe shine yaketa hanzarin ganin ya zuba Makuddan Kudade domin ginin Jami'a, zuba wadannan Makudan Kudade zai bashi damar ya Wazgi Percentage dinshi, amma baayi abun don Talakawa da "Ya "yansu ba, abunda zai tabbatarma Mai karatu da haka shine, Kasawar da Audu Yari yayi wajen bada gudumuwa da tallafi wajen habbaka Jami'ar Gwamnatin tarayya da mukeda ita anan garin Gusau, Sannan kuma wadancan jami'o'i daya ambata da cewa jihar Zamfara bata cike guragunta a cikin su to yanzu Mun cike sune?

Don haka duk Wani Soki burutsu da Audu Yari da Yaran Shi zasuyi akan Gina Jami'a Mallakar Gwamnatin jiha to bada gaske sukeyi ba Sai dai kawai Suna yaudarar kawunansu ne.

Alhamdulillah Matakan da Gwamnatin Hon. Dr Bello Matawallen Maradun Barden Hausa ke dauka na bunkasa Cigaban jihar Zamfara munada Gamsuwa dasu,  tun daga Kokarin Samarda tsaron lafiya da dukiyoyin Al'umma Wanda ya tabarbare a hannun Audu Yari, Samarda Shiraruwa na rage radadin fatara da yayi kaka-gida a lokacin Yari, kamar tallafin wata wata na Mata da ZASIP da sauransu.

Kula da hakkoka da bukatun Ma'aikata shima abun a yaba ne da dai sauran su.

Daga cikin illolinda Audu Yari yayi muna akwai rashin biyan albashi mafi karanchi na dubu goma sha takwas (18,000) har ya gama Mulkin Shi.

Haka Kuma, Saboda bakar keta irinta Audu Yari yasa bai biyama diyan Talakawa Kudin jarabawar kammala Sakandare (WAEC da NECO) domin Kada su shiga Jamia su zama wata tsiya.

Don haka Mun gamsu da abunda Gwamnati take akai nai yanzu, muna yimata fatar dorewa akan daidai.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA