BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MAI DARAJA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA HON DR BELLO MUHAMMAD MATAWALLEN MARADUN MON



Daga Alhajin APC




Salamun Alaikum.

Mai Girma Gwamna tareda Girmamawa da Mutumtawa nake rubuta maka wannan Wasika a matsayinka na Shugaban mu Wanda Allah ya jibantama nauyin Kare rayuwa, mutumci da dukiyoyin Al'ummar jihar Zamfara Samada mutum Miliyan Uku da doriya.

Mai Girma Gwamna a Lokacinda Allah ya baka jagorancin Wannan jihar, mutanen jiha sunyi murna da farin ciki Marar misaltuwa musamman mutanen Karkara wadanda sune sukafi Shafuwa da iftila'in dake addabar jihar Zamfara.
Tabbas Mai daraja Gwamna Al'ummar jihar Zamfara sunyi farin ciki da jawabinka na farko Wanda a cikin Shi ka nuna damuwarka akan abunda ke faruwa a yankunan jihar Zamfara da kuma irin Matakan daka dauka nayin Sulhu da "Yan bindiga, matakinda ya haifar da d'a Mai ido, Wanda har Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya yabama Wannan kokarin naka tareda jinjina maka tareda yin Kira ga takwarorinka Gwamnoni da Suyi koyi dakai ta wannan haujin.

Mai Girma Gwamna Saninka ne kuma Sanin al'ummar jihar Zamfara ne cewa wannan Matsalar ta rashin tsaro ka gajeta ne daga Gwamnatin data gabata ta Abdul Aziz Yari.

Mai Girma Gwamna tsohon Dan Siyasa Kake ba Sabon shiga ba, Kasan Sharrin Siyasa ka Kuma San amfanin ta, kasan hanyoyin da ake bi a samu cikakkiyar nasara  a Gwamnatance.

Mai Girma Gwamna yakamata ka tsaya kayi karatun tanatsu ka gano dalilanda sukasa Matsalar tsaro ke kokarin dawowa tattareda irin kokarin da kakeyi ba dare ba rana don ganin al'ummar birni da karkarar jihar Zamfara sunyi kwana da ido biyu ba tareda fargabar komai ba.

Mai Girma Gwamna Sanin Kane cewa a dabi'a ta Siyasa da "Yan Siyasa duk Wadanda baku jam'iyya daya dasu kuma baku hadu akan wata manufa ba to babu yadda za'ayi suyi maka fatar Samun nasara kowace irice.

Mai Girma Gwamna matukar bakayi amfani da karfin ikon da Allah ya baka ba wajen yin waje rod da "Ya 'yan jam'iyyar daba naka ba kuma bakuyi tarayya dasu wajen ceto jihar Zamfara ba to akwai yiyuwar Cigaba da fuskantar kalubale, (Allah Ya tsare, Allah Ya kiyaye).
Mai Girma Gwamna anyi Gwamnatoci baya Kafin Gwamnatinka a jihar Zamfara kuma kowa (har Kai) ya shedi yadda aka gudanarda Gwamnatocin, baa taba jam'iyyar Gwamnatin jiha daban ta Kananan hukumomi daban ba, ko lokacin Mulkin Yarima da akayi tare dakai, da Yarima yazo ya taradda Shugabannin Kananan hukumominda bana jam'iyyar Shi ba Saida ya Kare lagonsu Sannan yasamu ya zauna lafiya kuma ya kaucema kowace irin barazana ta Siyasa.

Mai Girma Gwamna ka saki jikinka kuma ka dogara ga Allah ka rabu da kaya don ka Samu nasarar tafiyarda Gwamnatin ka yadda yakamata tare kuma da cin nasarar Gwamnatinka.

Allah Ya taimakeka ya Kara maka kwazo da himma na ganin kuduroranka na alkhairi ga jama'ar jihar Zamfara sun tabbata, Allah Ya baka ikon yin nazari akan wannan wasikar tawa tare kuma da yin aiki da abunda ta kunsa.

Comments

  1. Gaskia wannnan shawara tayi sosai Allah yabashi ikon aiki da ita

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA