ABDUL'AZIZ YARI DA MAKAFIN MAGOYA BAYAN SHI NA SIYASA



Rubutawa: Mohammed Kabir (MK)

Fassarawa: Ibrahim Bello (Alhajin APC)

A duk Lokacinda naci Karo da wasu rubuce rubuce na "Ya 'yan jam'iyyar adawa a Jihar Zamfara, abun yana matukar daure mani Kai har inkasa fahimtar Ko cewa wai ko sunsan abunda ake cema adawa da matsayin yan adawa.

Ba da dadewa ba, Gwamna Bello Matawalle ya bada gargadi ga tsohon Gwamna Abdul Aziz Yari akan cewa duk ya kuskura ya shigo jihar Zamfara kuma ya kasance aka samu Yan bindiga sunkai hari a wani wuri, Shi Gwamnan da kanshi zai jagoranci jami'an tsaro a kamo Shi. 

Kafin wannan Jawabin nashi, Ya bayyana dalilanshi na daukar Wannan Matakin. Ya fahimci cewa duk Lokacinda Abdul Aziz Yari ya shigo a jihar Zamfara to dole Sai ka ji ankai hari Wani gari inda zaka taradda anyi hasarar rayuka da dama, Wanda yake cewa wannan abun dubawa ne ace duk ya shigo Sai wani abu ya faru a cikin jiha?

Abunda ya bani Mamaki, Naci Karo da wasu rubuce rubuce na wasu Makafin magoya bayan tsohon Gwamna wadanda suka dauke Shi tamkar Wani Karamin Ubangiji Suna kokarin mayarda martani ga Mai daraja Gwamna batareda wata kwakwkwarar hujja ba.

A matsayin ku na "Yan adawa, Kunada dama ku kalubalanci Manufofin Gwamnati amma kuma ba tareda tsallaka iyaka ba. Babu Wata Gwamnati wadda tasan abunda takeyi kuma ta rungume hannayenta ta bari wani ko wasu Ya Siyasantarda harkar tsaro a cikin yankin ta.

Yau dinnan, wani daga cikin na hannun damar tsohon Gwamna Abdul Aziz, Ibrahim Danmalikin Gidan Goga a Wani taro tareda Manema labarai, Danmaliki ya bayyana cewa akwai fiyeda Bindiga Miliyan hudu a hannun Yan ta'adda, ina ne Danmaliki ya samu wannan Kididdigar? Sannan ya akayi har yasan da kasancewar su?

La'akari da Maganganun su bayan kashedin da Gwamna Matawallen Maradun yayi, Kai tsaye zaka fahimci cewa ruwa basu tsami banza.

Addu'ar mu a koda yaushe itace Allah ya tona asirin duk Wani Mai hannu Ko kuma Mai kokarin ganin cewa yayi kutunguila ga Zaman lafiya a jihar Zamfara.
Ameen Ya Allah.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA