Ministan Yan Sanda Dingyadi da Sanata Wamakko da Tsohon Gwamna Yari na kitsa shirin haddasa rashin tsaro a Zamfara.
Daga Shafin Maniyarzamfara.com Tsohon gwamna Abdul'aziz Yari Abubakar a ran Larba ta wannan makon yayi wani taron sirri da Ministan Yan Sanda kasa Muhammadu Maigari Dingyadi tare da shugaban kwamitin tsaro Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a gidan Wamakko dake Asokoro, garin Abuja tare da manufar zargin da akeyi na neman a dauke Kwamishinan Yan Sanda na Jihar Zamfara Muhammadu Dangogo. Bayanin wata majiyar ta baiyana taron na sirri da aka mayar da sunan ziyara ga tsohon gwamna Wamakko yana da manufar hargitsa zaman lafiya na jihar Zamfara don cimma burinsu ga samun iko a matakin tsaro. Anji cewar tsohon gwamna Yari ya yiwa Ministan alkawalin tallafi da samar masa da wasu makudan kudade akan ya tabbatar da Sufeton Yan Sanda yabi umurninsa don dauke kwamishinan Yan Sanda tare da kawo nasu dake yanzu haka a hedikwatar Yan Sanda ta kasa bayan karin girman da akayi masa. Sanata Wamakko shine Shugaban kwamitin tsaro na Majalisar Dattawa yayin da ake zargin yana da hannu akan...