YADDA ZA'A SHIRYAR DA YARA DABI'U MASU KYAU


1. Ku dinga shiga gida da sallama, inda hali ku sumbanci yaran ku, wannan zai sa musu kauna da sanin kiman kan su.

2. Ku zama masu kyakkyawar mu'amala ga makwabtanku, kada ku zama masu gulma da rada, kar ku fadi munanan magana ga masu abin hawa a kan hanya.
Yaran ku suna ji, za su koya kuma zasu dauka su dinga yi.

 3. Duk lokacin da za kuyi magana da iyayen ku a waya ko za ku ziyarce su ku tabbatar kun yi tare da yaran ku, domin hakan zai sa yara su koyi jin ƙai da kuma tausaya muku don sun ga yadda kuke yi wa naku iyayen.

4. Lokacin kai su makaranta kar ku yawaita sa musu kide kide da waƙoƙin sharholiya, ku yawaita basu labarai da kissoshi da zai ankarar da su Al'amurra na gari, Ina tabbatar muku zai taimaka sosai!

5. Karanta musu guntayen labarai ko wani guntun tarihi a ko wane rana, ba zai ci lokaci ba amma yana taimaka musu wajen nitsuwa kuma yana kama zuciyar su.

6. Ku tsaftace kan ku da Wanka da wanke baki da taje kai da sa kyawawan tufafi (Kaya) ko da kuwa kuna zaune a gida ne ba inda zakuje, wannan zai koya wa yara tsafta da kwalliya ba sai za aje unguwa ba.

7. Kuyi kokari kar ku yawaita dorawa yaran ku laifi ko magana akan ko wani abu su kayi, ku koyi kawar da kai akan wasu abubuwan wannan zai taimaka musu wajen sa su samu nitsuwar kan su.

8. Ku nemi izinin shiga dakin yaran ku, kuma kada kawai ku kwankwasa ko yin sallama kawai, ku saurare su su baku izini kafin ku shiga, wannan zai sa suma suyi muku makamancin sa wajen shiga dakin ku.

 9. Ku nuna rashin jin dadin ku, ku nemi basu hakuri a duk inda ku kayi kuskure wannan zai koya musu zama masu ƙanƙan da kai da kuma masu sauƙin kai.

10. Kar ku me da magana ko shawarar yaran ku abun ƙyaliya ko yasashshiya ko abin wasa ko da kuwa bisa wasa kukayi domin yana kona musu rai.

11. Ku gwadawa yaran ku girmamawa da mutuntawa wannan yana da muhimmanci sosai a gare su don zai kara musu kaifin mutuntakar su da sanin darajar kan su.

12. Kar kuyi tsammanin zasu fahimci ko yarda da shawarwarin ku da farko, kada ku dauki hakan da zafi, ku bi a hankali da hakuri da jajircewa bukata za ta biya.

13. Ku dinga salloli da ibada tare da yaran ku, ku koyar da su ibada, wannan shine zai kai su ga nasara.

14. Bugu da kari, bayan sallar asuba ku tambayi yaran ku irin shirin da sukayi wa wannan rana na game da Al'amurran su na abinda ya shafi lokutan su, rashin haka yana iya sa su fada hannun lalatattun yara tsaran su kuma su bata musu tarbiyya.

15. Ku sumbance yaran ku duk safiya ku sa musu albarka.

Ku taimaka ku yada wannan don sauran Iyaye su karu su ma.

ALLAH TA'ALA YA ALBARKACE MU DA IYALANMU BAKI DAYA.AMIN

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA