YADDA KALAMAN TSOHON GWAMNA A.A. YARI SUKA RURA WUTA GABA TSAKANIN FULANI DA YAN- SAKAI.




Daga  Khalifa Ja'afar


Tun a ranar da Abdulaziz Yari yayi wata dogowar fira mai sa firgici a gidan Radion Kaduna a farkon shekar 2013, inda ya fadi cewa "dukkan kashe-kashe da sace-sace da a keyi a Zamfara fulani ne", hakika, wadannan kalamai sun rura wutar gaba tsakanin Fulani da 'yan sa-kai da sauran al' ummar jihar, domin daga wannan ranar ne fulanin dake zaune a Zamfara aka fara gasa masu aya a hannu, daga wannan ranar basu sake samun walwala da rayuwa mai kyau ba sai a wannan ranar sanadiyar maigirma gwamna, Honorable Bello Muhammad Mutawalle, duk wanda yake a Zamfara yau ya shedi hakan, domin a wannan ranar ne fulani suka samu shiga cikin al'umma kamar yada suka saba tare da gudanar da wasannin su na gargajiya wato (SHARU) a koina a fadin wannan jihar, suka hadu a babban birnin jiha garin Gusau domin gudanar da wannan wasa ta al'ada.

Ranar da Abdulaziz Yari ya furta wadannan kazaman kalaman a gidan rediyon Kaduna idan masu bibiyar rubutu na a wannan kafa ta social media ba su manta ba, a wannan ranar nayi Allah wadai da wadannan kalamai nashi saboda tunanin abinda wadannan kalamai za su iya janyowa ga rayuwar fulani dake zaune a wannan jiha, duk abinda nayi hasashe a wancan lokacin sai da ya tabbata, domin daga ranar ne 'yan sakai da sauran al' ummar gari suka fara nuna kyamar su karara ga duk inda suka ga bafulace matan su da mazan su, abin bai tsaya ga kyamatar su kadai ba, har sai da takai ga ana cin zarafin su tare da kisan su saboda wadannan kazaman kalamai da Abdulaziz Yari yayi akan su, wannan ne ya tunzura fulani ta hanyar hada kai da barayin dake kisan mutane, domin suna ganin hakan shine tsiratar da rayuwar su daga wannan musiba ta kyamar su da kisan su da aka fara a Zamfara, hakika a wancan lokaci sun zabi su hada kai da Barayi masu kisan mutane da su zauna ana yi masu kisan mummuke saboda zargin su da Yari ya saka a zuciyar al'umma.

Illar kalaman wannan tsohon gwamna, basu tsaya a Zamfara kadai ba, har sauran jihohin Nigeria sai da kalaman nan suka yi tasiri a wurin su, domin saida ta kai wurare kalilan ne kawai a wannan kasa fulani ke iya walwala a ciki, wadda wannan tsangwama da ake yi masu matukar ba a kauda ita ba kamar yada aka kawai da ita a Zamfara, lallai babu ranar da za a samu zaman lafiya da fulani a wannan kasa.

Hakika Zamfara mun yi sa'ar gwamna, wanda al'umma ne kawai a gaban shi ba tara dukiya ba, Allah ya dubi kyakkyawar manufar dake a cikin zuciyar wannan gwamna, shiyasa ya bashi nasarar da koda a cikin shikara hudu ya same ta dole duniya ta yaba mashi, amma abin mamaki sai ya sami wannan cikakkiyar nasara a cikin wata biyu kacal, Allah kai ne abin godiya.

Magauta sun yi suka sun yi zagon kasa na ganin a kowane hali Matawalle bai samu wannan nasarar ba, amma dayake Allah yana a cikin lamarin shi, sai ya cigaba da kunyata su a kowace rana, duk lokacin da wani daga cikin su ya fito yana soke-soke, sai al'umma su rika ganin shi wani irin sha-sha-sha wanda bai san ciwon kan sa ba, daga nan yakamata su gane cewa Matawalle fa Allah ne yake cikin lamarin shi, su kuma suna kokarin  shiga cikin sahun mutanen da Allah yake yaka domin takalo fushin shi da su kayi.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA