AJANDAR ABDUL'AZIZ YARI TA NEMAN ACE YAFI KOWA KUDI A JIHOHIN SOKOTO, KEBBI DA ZAMFARA TA BAYYANA A FILI.



Daga Ibrahim Bello Gusau.




Jihar Zamfara tana Daya daga Cikin Jihohin tarayyar Najeriya a Yankin arewa maso yamma Mai jihohi Bakwai, Jihar Zamfara tana Daya daga Cikin Jihohin da aka kirkiro a Shekarar 1996 a lokacin Mulkin Soja na Janaral Sani Abacha.

Daga Shekarar da aka kirkiro Jihar Zamfara Zuwa yau tayi Gwamnoni na farar Hula Guda hudu, wato:
Alh Ahmad Sani Yariman Bakura daga 1999-2007.

Alh Mahmoud Aliyu Shinkafi daga 2007-2011
Alh Abdul'aziz Yari daga  2011-2019
Alh Hon Dr Bello Matawallen Maradun Watan mayu 2019 Zuwa Yau.

Al'ummar Jihar Zamfara Sun Shedi Salon Mulkin Duk Wadannan Shugabannin Kuma zasu iya tarfa albarkacin bakinsu akan haka.

Salon Mulkin Yariman Bakura na tallafama Jama'a ne da neman suna a idon duniya.
Salon Mulkin MAS Kuma na Kokarin Gina Jihar Zamfara ne sai dai akwai Sakaci da ko inkula.
Salon Mulkin Abdul'aziz Yari na atara Kudi ne a hana al'umma Walwala tareda tauye su, Wannan shine ya kawo Girman Kai, Wulakanta Mutane da Rashin Sanin darajar Dan Adam wadda Allah Mahalicci yace "Hakika mun Karrama Dan Adam".

 AJANDAR ABDUL'AZIZ TA SON ACE YAFI KOWA KUDI A JIHOHIN SOKOTO, KEBBI DA ZAMFARA

Nau'in Salon Mulkin Abdul'aziz ba irin Wanda al'ummar Jihar Zamfara suka Saba dashi bane Kuma ba irin Salon Mulkin da suka gamsu dashi bane, Saboda al'umma sun kyamaci mutum Mai Girman Kai, dagawa, Wulakanta Mutane da Rashin Sanin darajar Dan Adam.
Ba a Banza ba Abdul'aziz yazo da irin Wadannan halayen ba, yazo da Wadannan halayen ne don ya samu ya Cimma manufar Shi son ganin ya zarta duk wani Mai dukiya a Yankin Zamfara, Sokoto da Kebbi da Kudi, shi yasa baida maice mashi yayi ko ya bari sai dai abunda ranshi yaso.

Abunda zai tabbatar maka da Wannan Ajandar Shine irin yadda Abdul'aziz ya jefa Jihar Zamfara Cikin Mugun bashi na kusan Biliyan 252 (Rahoton farko) Wadannan Kudaden zasu iya zarta haka idan rahoton Karshe ya fito (Allahu Aalam), ko Manyan jihohi irin su Legas da Kano baa taba lokacinda Gwamnatocin su masu barin gado suka bar masu bashin da yakai Quarter Trillion ba. Bashin da Abdul'aziz ya barma Jihar Zamfara ya zarta Quarter Trillion (Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un), Duk wadannan basosan ajanda ce ta son tara Kudi ta kowace irin hanya, Yaki-halas Yaki-haram (wal'iyazubillah).

Daga Karshe, Ina Addua ga Jihar mu ta Zamfara, Allah ya kawo muna dawwamammen Zaman lafiya da Wadatar arziki, Haka Kuma ina Addua ga Mai Girma Gwamna *Hon Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun* akan Allah yayi mashi jagoranci ga abunda a daidai Wanda zai Ciyarda Jihar Zamfara Gaba, Allah yayi mashi Kariya daga kowane irin Sharri, Haka Kuma ina adduar Allah ya taimaki Yan Kwamitin da aka dorama Binciken Gwamnatin data gabata a Karkashin Jagorancin H.E Malam Wakkala ya Basu ikon sauke nauyin da aka dora masu batareda wata fargaba ko tsoro ba, yayi masu kariya daga kowane irin Sharri.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA