LABARI DA DUMI-DUMI: AN KAMA KANIN SAKATAREN GWAMNATIN JIHAR ZAMFARA DA MILIYAN 60 DA BINDIGOGI A MOTA




Daga S. Sadiq, Gusau.




Yau Talata, Hukumar hana cin hanci da hana almuzaranci da dukiyar kasa wato EFCC ta kama kanin Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara wato Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi mai suna Murtala Muhammad a gidan shi mai lamba 145 na rukunin gidajen Igala dake babban birnin jihar Zamfara wato Gusau.


An kama shi da tsabar kudi Naira Miliyan Sittin (60,000,000), motar Toyota Landcruiser mai DKA 67 PX tare da bindigogi kirar waje guda biyu (2) tare da daya (1) kirar gida.



Hukumar zata gabata da shi gaban Kotu domin fuskantar hukunci.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA