BADAKALAR MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA


Daga S. Sadiq, Gusau.


A cigaba da dambarwar siyasar da ke faruwa a jihar Zamfara, 'Yan Majalisar dokokin jihar Zamfara masu goyon bayan Gwamnatin Jihar na cigaba da danne hakkokin 'Yan uwansu 'Yan Majalisa guda Bakwai (7) wadanda suka samu sabanin ra'ayi game da tsayar da 'Yan takarkarun zaben da ya gabata.

Duk da umurnin da Babbar Kotun Jihar Zamfara dake Gusau karkashin Justice Bello Gusau, Majalisar karkashin jagorancin Rt.Hon. Sanusi Garba Rikiji tayi fatali da wannan umurnin.

A binciken da Jaridar Tauraruwa tayi ya nuna cewa a satin da ya gabata ne Gwamnatin Jihar ta ba Majalisar dokokin jihar Takin zamani kamar yadda ta saba duk shekara amma dayan bangaren dake goyon bayan Gwamnatin suka rarrabe tsakanin su ba tare da sauran sun sani ba. Haka kuma a cikin satin duka  an raba masu kayan azumi wanda ya hada da Gero, Shinkafi, Sugar da dai sauran su amma shima din sun rarrabe tsakanin su.

Wakilin Tauraruwa yayi hira da wani Lauya me zaman kanshi, Barista Musa Ibrahim Kaura yace Majalisar dokokin jihar Zamfara karkashin jagorancin Sanusi Garba Rikiji tayi ma doka karantsaye wanda wannan ya kan iya jawo hukunci mai tsanani ga shugabannin Majalisar dokokin.

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA