BADAKALA A MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA: SHIN KO GWAMNA ABDULAZIZ YARI YANA DA MASANIYA?
Daga Sani Sadiq, Gusau.
Tun bayan watanni 7 da suka gabata aka shiga danbarwar siyasa a jihar Zamfara sanadiyar 'Yan takarar da Gwamna Abdulaziz Yari ya so ya tilasta su a kan jama'ar Zamfara wanda wasu gungun 'Yan takarar Gwamna su 8 suka yi tsaye na ganin hakan bai faru ba, siyasa jihar Zamfara ta dauki wani sabon salo da rikici.
Haka kuma cikin Majalisar dokokin jihar, an samu rarrabuwar kawuna inda wasu 'Yan Majalisar dokokin guda 7 suka mara ma wadannan 'Yan takarar Gwamna guda 8 baya na ganin cewa an tabbatar da adalci ga jama'a na tsaya masu da 'Yan takarar da jama'a suke so ba wanda Gwamnan ke so ya tsayar ba domin kare muradun shi.
A sanadiyar hakan yasa sauran 'Yan Majalisar dokokin masu goyon bayan Gwamna suka dauki mummunan matakin akan 'Yan uwansu guda 7 na korar su daga Majalisar tare da hana masu hakkokan su tun daga albashi, alawus da sauran su wanda hakan an yi shi ba bisa ka'ida ba.
Duk da umurnin da wata babban Kotun Jihar dake Gusau babban birnin jihar ta ba Majalisar dokokin jihar na cewa 'Yan Majalisar dokokin guda 7 da suka dakatar basu dakatu ba kuma a cigaba da bayan su hakkokan su amma Majalisar dokokin karkashin jagorancin Rt Hon Sanusi Garba Rikiji tayi fatali da wannan umurnin inda ta ruke kudin wadannan 'Yan Majalisar su 8 har kimanin kudi Naira Miliyan Dari da Hamsin (N150,000,000).
Binciken da jaridar Tauraruwa tayi ya nuna cewa wadannan kudin da aka hana ma wadannan'Yan Majalisar dokokin guda 8 ba'a maidasu a cikin asusun Gwamnati ba ana zargin Kakakin Majalisar dokokin wato Rt Hon Sanusi Garba Rikiji tare d Shugaban masu rinjaye a Majalisar dokokin wato Hon Isah Abdulmumini T/Mafara da rikewa tare da amfani da kudin.
Amma abun tambaya anan shine, shin Gwamna Abdulaziz Yari ya san da wannan badakalar dake faruwa a Majalisar dokokin jihar Zamfara kuwa? Koma minene amsar wannan tambayar, lokaci ne zai nuna.
Comments
Post a Comment