AN HANA ZABABBUN 'YAN MAJALISAR TARAYYA TARE DA 'YAN MAJALISAR DOKOKI NA JIHAR ZAMFARA HALARTAR TARON BITA




Daga Aliyu B. Musa, Abuja.

 Kasancewar ya zama dabi'a a duk lokacin da aka yi sabon zabe aka samu sababbin wakilai, akan shirya masu wata bita ta sanin makamar aiki wanda manyan 'Yan Majalisar dattijai da wakilai ta kasa sukan halarta a babban dakin taro na kasa wato National Conference Hall dake Abuja.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa wato INEC ke tura sunayen wadanda suka ci zabe amma ba sunayen wadanda suka fito daga jihar Zamfara.

Binciken da jaridar Tauraruwa tayi ya nuna cewa a yayin da sauran zababbun 'Yan Majalisar Tarayya da na jiha suke nasu taron bita a Babban Zauren taro na kasa dake Abuja su kuma takwarorin su na Jihar Zamfara da ba'a ba damar shiga babban zauren ba suna wani Otal mai suna Stonhedge dake babban birnin tarayya wato Abuja.



Idan baku manta ba kungiyar gwamnonin Najeriya ma sun taba shirya wani taron bita ga tsofaffi tare da sababbin zababbun Gwamnoni inda gwamnan jihar Zamfara yaje tare da Alhaji Muktar Idris a matsayin zababben gwamna duk da Kotun daukaka kara dake Sokoto ta aje hukuncin babbar Kotun Jihar Zamfara da tayi na halattar da zaben fidda gwani da Gwamnatin take ikirarin tayi. Wannan yasa masana daga kowane bangare na Najeriya suka dunga suka akan cewa anyi wa Doka karantsaye na halartar shi Alhaji Muktar Idris wajen taron.

Hana su da akayi bai rasa nasaba da maganganu da sukayi ta kawo akan ganin yadda Gwamna Abdulaziz Yari yake ma dokokin Najeriya karan tsaye.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA