Posts

Showing posts from May, 2019

LABARI DA DUMI-DUMI: AN KAMA KANIN SAKATAREN GWAMNATIN JIHAR ZAMFARA DA MILIYAN 60 DA BINDIGOGI A MOTA

Image
Daga S. Sadiq, Gusau. Yau Talata, Hukumar hana cin hanci da hana almuzaranci da dukiyar kasa wato EFCC ta kama kanin Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara wato Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi mai suna Murtala Muhammad a gidan shi mai lamba 145 na rukunin gidajen Igala dake babban birnin jihar Zamfara wato Gusau. An kama shi da tsabar kudi Naira Miliyan Sittin (60,000,000), motar Toyota Landcruiser mai DKA 67 PX tare da bindigogi kirar waje guda biyu (2) tare da daya (1) kirar gida. Hukumar zata gabata da shi gaban Kotu domin fuskantar hukunci.

BADAKALAR MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA

Image
Daga S. Sadiq, Gusau. A cigaba da dambarwar siyasar da ke faruwa a jihar Zamfara, 'Yan Majalisar dokokin jihar Zamfara masu goyon bayan Gwamnatin Jihar na cigaba da danne hakkokin 'Yan uwansu 'Yan Majalisa guda Bakwai (7) wadanda suka samu sabanin ra'ayi game da tsayar da 'Yan takarkarun zaben da ya gabata. Duk da umurnin da Babbar Kotun Jihar Zamfara dake Gusau karkashin Justice Bello Gusau, Majalisar karkashin jagorancin Rt.Hon. Sanusi Garba Rikiji tayi fatali da wannan umurnin. A binciken da Jaridar Tauraruwa tayi ya nuna cewa a satin da ya gabata ne Gwamnatin Jihar ta ba Majalisar dokokin jihar Takin zamani kamar yadda ta saba duk shekara amma dayan bangaren dake goyon bayan Gwamnatin suka rarrabe tsakanin su ba tare da sauran sun sani ba. Haka kuma a cikin satin duka  an raba masu kayan azumi wanda ya hada da Gero, Shinkafi, Sugar da dai sauran su amma shima din sun rarrabe tsakanin su. Wakilin Tauraruwa yayi hira da wani Lauya me zaman kanshi, Bari...

AN HANA ZABABBUN 'YAN MAJALISAR TARAYYA TARE DA 'YAN MAJALISAR DOKOKI NA JIHAR ZAMFARA HALARTAR TARON BITA

Image
Daga Aliyu B. Musa, Abuja .  Kasancewar ya zama dabi'a a duk lokacin da aka yi sabon zabe aka samu sababbin wakilai, akan shirya masu wata bita ta sanin makamar aiki wanda manyan 'Yan Majalisar dattijai da wakilai ta kasa sukan halarta a babban dakin taro na kasa wato National Conference Hall dake Abuja. Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa wato INEC ke tura sunayen wadanda suka ci zabe amma ba sunayen wadanda suka fito daga jihar Zamfara. Binciken da jaridar Tauraruwa tayi ya nuna cewa a yayin da sauran zababbun 'Yan Majalisar Tarayya da na jiha suke nasu taron bita a Babban Zauren taro na kasa dake Abuja su kuma takwarorin su na Jihar Zamfara da ba'a ba damar shiga babban zauren ba suna wani Otal mai suna Stonhedge dake babban birnin tarayya wato Abuja. Idan baku manta ba kungiyar gwamnonin Najeriya ma sun taba shirya wani taron bita ga tsofaffi tare da sababbin zababbun Gwamnoni inda gwamnan jihar Zamfara yaje tare da Alhaji Muktar Idris a matsayin z...

BADAKALA A MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA: SHIN KO GWAMNA ABDULAZIZ YARI YANA DA MASANIYA?

Image
Daga Sani Sadiq, Gusau. Tun bayan watanni 7 da suka gabata aka shiga danbarwar siyasa a jihar Zamfara sanadiyar 'Yan takarar da Gwamna Abdulaziz Yari ya so ya tilasta su a kan jama'ar Zamfara wanda wasu gungun 'Yan takarar Gwamna su 8 suka yi tsaye na ganin hakan bai faru ba, siyasa jihar Zamfara ta dauki wani sabon salo da rikici. Haka kuma cikin Majalisar dokokin jihar, an samu rarrabuwar kawuna inda wasu 'Yan Majalisar dokokin guda 7 suka mara ma wadannan 'Yan takarar Gwamna guda 8 baya na ganin cewa an tabbatar da adalci ga jama'a na tsaya masu da 'Yan takarar da jama'a suke so ba wanda Gwamnan ke so ya tsayar ba domin kare muradun shi. A sanadiyar hakan yasa sauran 'Yan Majalisar dokokin masu goyon bayan Gwamna suka dauki mummunan matakin akan 'Yan uwansu guda 7 na korar su daga Majalisar tare da hana masu hakkokan su tun daga albashi, alawus da sauran su wanda hakan an yi shi ba bisa ka'ida ba. Duk da umurnin da wata babb...