TSAKANIN ABDULAZIZ YARI DA EFCC (KASHI NA DAYA)



Daga Shehu Ibrahim.




Nayi kicibis da rubutun mai ba gwamnan Zamfara  Abdulaziz Yari Abubakar mai taimak mashi akan yada labarai wato Hon Ibrahim Dosara akan martani da ya bayar akan rahoto na wasu jaridu da sukayi na cewa Hukumar yaki da sata da almubazzaranci da kudaden gwamnati wato EFCC tayi na cewa ta hada kwamitin da zai binciki gwamnoni guda uku wanda shi gwamnan jihar Zamfara na daya daga cikin su.

Abun mamaki na anan shine, yadda Hon Dosara ya yi tsayuwar gwamin jaki na kokarin karyata labarin da wadannan manyan jaridun suka rubuta, wanda duk wani mazauni jihar Zamfara yayi hasashen hakan zata faru da Gwamna Abdulaziz Yari mai barin gado.

Akwai abubuwa da dama da suka faru a cikin gwamnatin shi wanda mutanen Zamfara sheda ne akan haka. Na farko kudin bailout da Mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari Ya basu domin walwale matsalolin ma'aikata a jiharhar yanzu ba wanda zai nuna ina aka sa wadannan kudade kasancewar ma'aikatan Zamfara sune mafi amsar kankancin albashi a duk fadin Najeriya.

A shekarun baya da suka wuce, Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa Gwamnan Zamfara ya sayi wani Otal mai hawa bakwai a Jihar Legas wanda shi Gwamnan bai musanta hakan ba.

Akwai wasu makudan kudin da aka wawure daga cikin asusun gwamnatin Jihar Zamfara domin biyan bashin da ake bin shi gwamnan ba na Jihar Zamfara ba wannan avune wanda yake bayyane a idanun duniya.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA