KA TSAYAR DA YAN TAKARAR MU KO MUKI BAKA ƘURI'UN MU: GARGADIN GWAMNATIN JIHAR ZAMFARA ZUWA GA BUHARI
Daga S. Sadiq, Gusau.
Sakamakon rikita-rikitar da ake ciki na rashin samun Yan takarar jam'iyyar APC a Jihar Zamfara ta dauki sabon salo inda jami'an gwamnatin suka yanke hukuncin ba zasu zabi shugaba mai ci yanzu ba wato Buhari in har bai tsayar masu da Yan takarar su ba.
Alamu sun nuna haka ne a lokacin da aka shirya zaben Shugaban Kasa yare da na Yan Majalisun tarayya inda bayanai sirri suka nuna an turo da kudin da ya kamata a ba wadanda zasu wakilci Jam'iyyar a runfunan jefa kuri'a amma gwamnan ya hana a baryar da kudin.
Bayanan da muka samu game da kudin shine gwamnan ya bukaci da a bashi kudin a hannu ba tare da an tura su ga asusun ajiya na Jam'iyyar APC ba Amma hakan bai samu ba sai dai aka tura a asusun ajiya na Jam'iyyar APC.
Yanzu haka dai shugabannin Jam'iyyar APC a bangaren gwamnati suna nan suna ganawar sirri tun daga matakin mazabu har zuwa na jiha domin ganin yadda zasu bullo ma zaben da za'a yi ranar Asabar 23/2/2019 kasancewar Hukumar Zabe mai zaman kanta wato INEC taki ta karbi sunayen Yan takarar jam'iyyar APC a reshen Jihar.
Comments
Post a Comment