BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA GWAMNAN JIHAR ZAMFARA MALAM ABDUL'AZIZ YARI




Daga Datti Assalafiy





Assalamu Alaikum.
Da farko ina yiwa Maigirma Gwamna jaje bisa abinda yake faruwa a jihar Zamfara kuma a matsayinka na babban jami'in tsaro na jihar Zamfara, wannan itace hanyar da Datti Assalafiy zai iya baka wasu shawarwari na tsaro wanda za'abi a magance matsalar da yake faruwa da taimakon Allah
Abin tsoro ne duk ranar da na ziyarci wannan dandali na facebook sai na ga sanarwa anyi garkuwa da mutane a Zamfara, yanzu matsalar ta fara shigowa har Katsina

Maigirma Gwamna ina son ka san da cewa manyan kungiyoyin 'yan bindigar da suka addabi Jihar Zamfara sun samu nasara kulla alaka na kasuwanci tsakaninsu da 'yan ta'addan jejin Sambisa, dama tun shekaraun baya jagoran 'yan ta'addan ya taba neman hanyar da zai kulla alaka dasu bai samu ba sai a yanzu

Kafin wannan alaka na kasuwanci ta kullu 'yan bindigar da suka mamaye Jihar Zamfara sai sun tafi har kasar Libya kafin su sayo bindiga da hardashin bindiga, kuma da tsada suke samu, ga tsadar kudin da suke kashewa kafin su tsallakewa shingen jami'an tsaro, amma a halin yanzu suna samun hanyar sayen bindiga da harsashi kai tsaye a gurin 'yan ta'addan Sambisa, bincikenmu ya tabbatar mana da cewa akwai wani kwamandan 'yan ta'addan jejin sambisa da aka ware a matsayin wanda zai dinga sayarwa 'yan bindigar jihar Zamfara makami, kuma da araha ake sayar musu, saboda 'yan ta'adda sun tara makami yanzu sun mayar da harkan hanyar cinikin makamai

Yawan bindigogin da yake hannun 'yan bindigar da suka addabi Zamfara ya wuce tunanin duk wani mai tunani a duniyar nan, sannan a ilmin tsaro da dabarun magance ayyukan ta'addanci da muka karanta kuma muke nazarinsu shine matsalar garkuwa da mutane mataki uku ne, akwai mataki na farko, da na biyu da kuma na uku, idan an kai mataki na uku ta lalacewar ta kai karshen lalacewa, to yanzu a Zamfara an kai mataki na uku a aikata lafin garkuwa da mutane, har ma abin ya fara shafan jihar Katsina, kuma matakannan guda uku kowanne da bayaninsa da bayanin hanyoyin da akebi a dakileshi da taimakon Allah

Maigirma Gwamna na samu labarin kana kokarin samar da matasa 'yan sa kai wato Civilian-JTF wanda duk wata zaka dinga biyansu naira dubu 15,000 domin su magance matsalar tabarbarewan tsaron jihar Zamfara saboda dukkan alamu ya nuna ka fitar da tsammani ga sojoji da 'yan sandan Nigeria, amma abinda nakeso ka fahimta shine yanzu haka kungiyoyin 'yan bindigar da suka addabi jihar Zamfara kalilan ne daga cikinsu suke amfani da bindiga kirar AK47 sai dai AK49 da Machine-gun, wanda 'dan sandan Nigeria ba'a masa horo da ya sarrafa Machine-gun ba ma sai AK47 kadai, to ina kuwa 'dan sa kai wanda bai san yadda ake sarrafa AK47 ba?

Kuma kamar yadda nace gurkuwa da mutane mataki uku ne, idan ya kai mataki uku to al'amari ya lalace, diban wadannan matasa da gwamna kace zakayi kuskure ne, domin zasu jefa rayuwarsu cikin halaka ne kai tsaye, amma ina mafita?

Mafita shine rundinar sojin Nigeria da na 'yan sanda wadanda suke aiki a Zamfara su binciki kansu, sannan su kara shiri, a nemi manyan ofisoshi jarumai a basu jagorancin yakin, don gaskiya ya bayyana cewa an kasa kare rayukan 'yan Zamfara, kuma me yasa jami'an tsaron gwamnati suka gaza har gwamna yayi zuciya yace zai samar da matasa suyi? babban dalili shine zan iya cewa they are ill motivated, kuma basu da capacity na tunkarar wadannan mutane, don idan ya zamto jami'in tsaro bashi da karfin da zai iya tunkarar 'dan bindiga suyi gaba da gaba kaga ai basu da amfani

Shiyasa nace dole a zakulo kwararrun jami'an tsaro daga bangaren soji da 'yan sanda jarumai masu ilmi a kan tsaro wadanda basu da tsoro, idan an tashi sai a raba jihar Zamfara kashi-kashi ta bangaren kananun hukumomin da 'yan bindigar suka mamaya, sai a ware kamar misali karamar hukuma guda daya ko biyu suna karkashin kulawar kwararren jami'in tsaro guda daya da zai jagoranci yakin, sai kuma a ware masa jami'an tsaro masu jini a jika kamar jami'ai 300, wancan karamar hukumar ma ayi haka, haka duk sauran kananun hukumomin da abinda ya ta'azzara ayi haka, sai ace wa kwamandojin bama son mu kara jin anyi garkuwa da wani mutum a yankin ka

Bangaren soji da 'yan sanda suyi wannan, gwamnatin jihar Zamfara ta basu isasshen alawus da lafiyayyun motoci, sai a basu lokaci kamar watanni biyu zuwa uku su shiga duk wani jeji da yake yankin da aka ware wa kowanne daga cikin kwamandojin a gani idan ba'a karya lagon wadanann tsageru 'yan bindiga masu garkuwa da mutane ba, kuma ya kasance gwamnatin tarayya ta tallafawa gwamnatin jihar Zamfara wajen biyan jami'an tsaron isasshen alawus da kayan aiki

Sannan gwamna kayi amfani da damarka wajen rokon gwamnatin tarayya ta tsaya tayi nazari duk wata hanya da aka tabbatar 'yan bindigar Zamfara suna bi suna samun makamai a hannun 'yan ta'addan jejin Sambisa abi a toshe, kuma tunda ya kasance 'yan bindigar kungiyoyi ne to dole sai an samu kwararrun jami'an tsaro na sirri (Intelligence) da 'yan leken asiri (spy) wanda su kuma zasuyi aikin hada kungiyoyin 'yan bindiga da suka mamaye jejin Zamfara rikici fada a tsakaninsu, idan suka fara rikici da fada a tsakaninsu to zasu tarwatsa kansu, su fara fallasa asirin junansu, to wannan zai taimakawa jami'an tsaro su dinga bugesu cikin sauki, hanyoyin da za'abi a hada kungiyoyin 'yan bindigar rikici da fada a tsakaninsu sirri ne, ku neme mu ta sirri mu baku satar amsa

Nazarin da kwamitin tsaro na majalisar dinkin dinkin duniya tayi akan illolin garkuwa da mutane a duniya shine yana daga cikin illarsa haifar da mummunan karayar tattalin arzikin kasa, wallahi inda jama'a zasuji bayanin illolin to da sai mun dena komai mun zafafa wajen yin kira ga gwamnati domin a yaki duk wata matsala na garkuwa da mutane a kowani yanki da ke wannan kasa tamu Nigeria

Muna rokon Allah Ya kawo karshen 'yan bindiga a jihar Zamfara
Allah Ka bawa shugabanninmu ikon aiwatar da shawarwarin da ake basu Amin

Comments

Popular posts from this blog

MUKTAR IDRIS KO SANUSI RIKIJI: AN SAMU RARRABUWAR KAWUNA A CIKIN MAGOYA BAYAN GWAMNATIN ZAMFARA

BA SHARRI BANE: GA CIKAKKEN BAYANIN ABUN DA YA FARU

WANI TSOHON DANMAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA YAYI WA TSOHON GWAMNA SUJADA